in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kira taron koli na kungiyar SCO a birnin Qingdao
2018-06-10 15:13:01 cri



Yau Lahadi, aka kira taron koli na kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO karo na 18 a birnin Qingdao dake gabashin kasar Sin, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron tare da bada jawabi mai taken "Yada Ruhin Shanghai domin raya makomar bil'adama ta bai daya". A cikin jawabin nasa, Shugaba Xi ya nuna yabo kan yadda kungiyar SCO ta samu manyan nasarori a cikin wadannan shekaru 17 da suka gabata tun bayan kafuwarta, sa'an nan ya yi kira ga bangarori daban daban da su kara yada Ruhin Shanghai domin warware matsaloli a halin yanzu, da kawar da hadarori da kalubalolin da ake tinkara. Bugu da kari ya nuna fatansa na ganin shugabannin kasashe mambobin kungiyar SCO sun hada kansu cikin sahihanci bisa Ruhin Shanghai, a kokarin raya makomar kungiyar ta bai daya.

Sakamakon ci gaban kungiyar hadin kai ta Shanghai SCO a cikin wadannan shekaru 17 da suka gabata tun bayan kafuwarta, kungiyar ta riga ta zama wata kungiyar shiyya-shiyya da ta shafi yankunan kasashe mafiya fadi da mutane mafiya yawa, adadin tattalin arzikin kasashe mambobin kungiyar ya kai 20% bisa na duniya, yayin da yawan mutanensu ya kai kimanin 40% bisa na duniya. Kungiyar ta kasance wani muhimmin bangare wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da ci gaba da ma kiyaye adalci a duniya baki daya.

Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, kungiyar SCO ta kafa wata dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, wadda ba'a kulla kawance da juna ba, sannan babu yin adawa da juna, kana ba'a daukar matakai kan wani bangare. A ganinsa, wannan ya kafa wani sabon tsarin hadin kai na shiyya-shiyya. Xi yana mai cewa,

"Dalilin da yasa a koda yaushe kungiyar SCO take da karfin hadin gwiwa sosai shine, saboda kungiyar ta gabatar da Ruhin Shanghai da kuma aiwatar dashi yadda ya kamata, wanda ya kunshi amincewar juna, moriyar juna, zaman daidai wa daida, yin shawarari, girmama tsarin al'adu daban daban domin neman samun ci gaba tare. A ganin Shugaba Xi, ruhin ya kawar da tsoffin ra'ayoyi na wanzuwar sabani a tsakanin al'adu daban daban, da yin yakin cacar baki, da ma yin takara ba tare da hadin kai ba. Don haka ruhin ya bude wani sabon shafi na dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, ganin yadda ya samu karbuwa daga gamayyar kasashen duniya."

Ban da wannan, Xi Jinping ya nuna cewa, kungiyar SCO zata kara yada Ruhin Shanghai domin warware matsaloli na halin yanzu, da kawar da hadarori da kalubalolin da ake fuskanta. Sa'an nan ya gabatar da ra'ayoyinsa biyar. Ya ce,

"Ya kamata mu kafa ra'ayin neman bunkasuwa da yin kirkire-kirkire da bude kofa ga ketare cikin adalci, amma ba tare da gurbata muhalli ba. Ya kamata mu tabbatar da ra'ayin neman tsaro dake kunshe da bangarori daban-daban kuma cikin dogon lokaci. Ya kamata mu kafa ra'ayin yin hadin-gwiwa irin na bude kofa ga juna, da yin mu'amala da kawowa juna moriya. Ya kamata mu kafa ra'ayin al'adu mai adalci da yin koyi da shawarwari da juna. Bugu da kari, ya kamata mu kafa ra'ayin tafiyar da harkokin duniya da yin shawarwari da hadin-gwiwa tare da juna."

Shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, ya kamata kasashe membobin kungiyar SCO su zama tsintsiya madaurinki daya wajen raya makomar al'umma ta bai daya. Shugaba Xi ya ce:

"Ya kamata a sa himma wajen tabbatar da shirin hadin kai na shekarar 2019 zuwa 2021 na murkushe masu tsattsauran ra'ayin addini, da 'yan a-ware na al'umma, da kuma 'yan ta'adda na duniya, da ci gaba da gudanar da atisayen yaki da ayyukan ta'addanci mai suna 'Peace Mission', da karfafa hadin kai a fannonin tsaron kasa, zartas da dokoki, da tsaron musayar bayanai. Nan da shekaru uku masu zuwa, kasar Sin zata horas da ma'aikatan kiyaye doka da oda dubu biyu ga bangarori daban-daban na kungiyar SCO, a wani kokari na inganta karfin zartas da doka da oda."(Kande,Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China