in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta kaddamar da kididdiga a fannin aikin gona
2018-06-10 14:05:45 cri
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya kaddamar da shirin kidaya a fannin aikin gona wanda za'a gudanar a duk fadin kasar da nufin tattara cikakkun alkaluma don gabatarwa shirin bunkasa aikin gona na kasar.

Shirin na hadin gwiwa ne tsakanin hukumar kididdiga da ma'aikatar samar da abinci da aikin gona ta kasar Ghanan, tare da tallafin shirin hukumar samar da abinci da raya aikin gona ta MDD (FAO).

Akufo-Addo ya tabbatarwa al'ummar kasar ta Ghana cewa, gwamnati za ta kammala aikin kidayar a shekarar nan ta 2018 domin inganta tsarin kididdigar aikin gona na kasar baki daya.

Ya ce kididdigar zata kasance wani muhimmin al'amari wanda za'a dinga gudanar da shi a kai a kai a kasar baki daya, ya kara da cewa, muddin kasar ta yi watsi da aikin gona za ta iya fadawa cikin garari kasancewar bangaren shine babban abinda kasar Ghanan ke alfahari dashi wajen cigabanta.

Akufo-Addo ya ce, gwamnatinsa ba za ta taba yin watsi da aikin gona ba. Akwai bukatar bunkasa aikin gona zuwa wani babban matsayi domin inganta rayuwar al'ummar kasar.

Rabon da kasar Ghana ta gudanar da aikin kidayar aikin gonar tun shekaru 33 da suka gaba, sai dai tana fata wannan kidayar ta shekarar 2018 zata kasance a matsayin wani sabon tsarin da zata yi amfani da shi cikin shekaru 10 masu zuwa. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China