in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#Taron SCO#Xi Jinping: Sin ta bullo da matakai da dama don raya makomar bil'adama ta bai daya ta kungiyar SCO
2018-06-10 12:18:21 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Lahadi cewa, domin raya makomar bil'adama ta bai daya ta kungiyar SCO, nan da shekaru uku masu zuwa, kasar Sin za ta horas da ma'aikata masu kiyaye doka da oda dubu biyu, da horas da mutane dubu uku kan ilimin daukar ma'aikata ga kasashe membobin kungiyar SCO, da kuma goyon-bayan gina yankin gwaji na hadin-gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kungiyar SCO a birnin Qingdao, da kafa kwamitin kula da dokoki na Sin da SCO. Haka kuma, kasar Sin za ta bada rancen kudi da ya kai Yuan biliyan 30 a karkashin tsarin gamayyar bankuna na kungiyar SCO, a wani kokari na samar da hidimar hasashen yanayi ga bangarori daban-daban.(Murtala Zhang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China