in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#Taron SCO#Xi Jinping ya bada shawarwari 5 kan makomar bai daya ta SCO
2018-06-10 12:13:36 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Lahadi ya bayyanawa shugabannin kasashe mambobin kungiyar SCO dake halartar taron kolin kungiyar a Qingdao cewa, ya kamata a kafa makomar bai daya ta SCO, da inganta kafa sabuwar dangantakar kasa da kasa. Game da haka ya bada shawarwari guda biyar, na farko ya ce kamata ya yi a karfafa hadin kai da nuna amincewar juna, da tabbatar da Sanawar Qingdao a dukkan fannoni, da yarjejeniyar hadin kai ta abokantaka da makwabtaka da kuma sauran takardu, kana da yin la'akari da moriyar sauran bangarori, da neman ra'ayoyi iri daya ba tare da yin la'akari da abubuwan da ake da banbance banbance a kansu ba, don karfafa hadin kai a tsakanin kungiyar ta SCO. Na biyu, ya kamata a sa himma wajen tabbatar da shirin hadin kai na shekarar 2019 zuwa 2021 na murkushe masu tsattsauran ra'ayin addini, da 'yan aware na al'umma, da 'yan ta'adda na duniya, kana da karfafa hadin kai a fannonin tsaron kasa, zartas da dokoki, da tsaron sadarwa, da nufin aza harsashi mai kyau na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Na uku, kamata ya yi a inganta hadin kai na neman samun ci gaba tare bisa manyan tsare-tsare, da karfafa karfin neman samun wadata tare. Na hudu, ya kamata a kafa gadar karfafa hadin kai da cudanya a fannin al'adu. Na biyar shi ne, a shirya wani tsarin hadin kai a tsakanin kasa da kasa tare. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China