in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#Taron SCO#Xi Jinping: ya kamata a fahimci yanayin da ake ciki a duniya
2018-06-10 12:11:05 cri
A yayin da yake halartar taron shawarwarin wanda ya kunshi bangarori daban-daban a yau Lahadi a wajen taron kolin kungiyar SCO a birnin Qingdao na kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping ya jaddada cewa, ya zama dole a kara fahimtar yanayin da ake ciki game da bunkasuwar duk fadin duniya baki daya. Xi ya ce, duk da cewa wasu kasashe na ci gaba da nuna ra'ayin nuna karfin iko ta hanyar siyasa, amma kada mu yi watsi da muradun kasashe daban-daban na kara tabbatar da zaman lafiya da bin doka da oda cikin adalci a duk duniya. Duk da kasancewar ana kara fuskantar barazanar tsaro iri daban-daban, amma babu tantama karfin ikon na kiyaye zaman lafiya zai iya magance barazanar rashin zaman lafiyar da ake fuskanta. Haka kuma, duk da cewa wasu kasashe na kara bin tsarin ra'ayin bangare guda da nuna ra'ayin bada kariya ga harkokin kasuwanci a duniya, amma inganta yin mu'amala da hadin-gwiwa da neman samun moriya tare tsakanin kasashe daban-daban ita ce makomar duk duniya. Bugu da kari, duk da cewa wasu mutane na ikirarin cewa al'adu mabambanta na cin karo da juna, amma kasancewar al'adu iri-iri shi ne babban karfin ci gaban bil'adama, kana, yin musanyar al'adu babban buri ne na al'ummar kasashe daban-daban.(Murtala Zhang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China