in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijer ta rattaba hannu kan yarjejeniyar ciniki marar shinge na nahiyar Afrika
2018-06-10 09:42:52 cri
Jamhuriyar Nijer ta sanya hannu kan takardun kungiyar tarayyar Afrika AU na yarjejeniyar ciniki marar shinge tsakanin kasashen nahiyar Afrika wato (AfCFTA) a takaice.

Da yake amsar takardun a ranar Jumma'a, shugaban gudanarwar AU, Moussa Faki Mahamat, ya bukaci ragowar mambobin kasashen wadanda har yanzu ba su sanya hannu kan yarjejeniyar ba da su hanzarta amincewa da yarjejeniyar ta AfCFTA.

Mahamat ya kuma bukaci mambobin kasashen da su sanya hannu da kuma amincewa da ka'idojin ba da damar zirga zirgar al'ummar nahiyar cikin 'yanci a tsakanin kasashen, da 'yancin bada izinin zama, da kuma 'yancin yin hadin gwiwa a fannin kasuwar sufurin jiragen saman Afrika (SAATM), wanda ya bayyana su da cewar suna da muhimmanci wajen daga martabar nahiyar ta Afrika.

A watan Maris, kimanin mambobin kasashen kungiyar AU 44 ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar AfCFTA a lokacin taron kolin AU a Kigali na kasar Rwanda, kana kasashe 31 suka rattaba hannu kan daftarin yarjejeniyar da ta shafi zirga zirgar mutanen nahiyar cikin 'yanci, da 'yancin izinin zama da kuma 'yancin kafa tsarin cinikayya na bai daya.

Ana bukatar a kalla kasashen 22 su amince da yarjejeniyar ta AfCFTA kafin ta zama cikakkiyar yarjejeniya, yayin da ake fatan amincewa da yarjejeniyoyi 15 da suka shafi 'yancin zirga zirgar al'ummar nahiyar, da 'yancin bada izinin zama, da kuma na kafa tsarin kasuwar sufuri ta bai daya.

Kawo yanzu, kasashe 4 da suka hada da Ghana, Kenya, Nijer, da Rwanda sun riga sun amince da yarjejeniyar ta (AfCFTA).(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China