A cewar UNICEF, babu isassun matakan kula da zirga-zirga tsakanin iyakoki dake kare yara daga hadarun da za su iya fuskanta, da suka hada da safararsu da azabtarwa da cin zarafi da kuma tsarewa.
A cewar kakakin hukumar UNICEF kan batun kaura Sarah Crowe, suna ganin yadda ake kara tsaurara matakan tasa keyar 'yan gudun hijira daga Turai da arewacin Afrika.
Tun daga watan Nuwamban bara, sama da 'yan yammancin Afrika 8,000 ciki har da yara 2,000 ne suka koma Niger daga Algeria, yayin da aka mayar da wasu 'yan gudun hijira da masu neman mafaka 900 dake da rejista 'yan asalin kasashen gabashin Afrika, zuwa Niger daga Libya. (Fa'iza Mustapha)