in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yankin yammacin Afrika na bukatar managartattun matatu don cimma bukatun kasuwanni
2018-06-09 15:22:44 cri
Wani kwararre kan harkar man fetur Alex Mould, ya ce yankin yammacin Afrika na bukatar matatar mai da za ta iya tace a kalla ganga miliyan 2 na danyan man fetur a kowace rana, domin cimma bukatun kasuwanni na albarkatun man fetur cikin gajeren lokaci.

Da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua yayin wani taron kasa da kasa kan man fetur na Ghana, Alex Mould, wanda kuma shi ne tsohon shugaban hukumar man fetur ta kasar, ya jadadda bukatar gwamnatoci a yankin, su samar da kyakkyawan yanayin da zai bada damar karfafa zuba jari a bangaren matatun mai don cimma bukatun kasuwanni.

Ya ce ya kamata a duba yuwar samun matatar mai da za ta iya tace gangar mai miliyan 2 a kowace rana, kuma idan yankin ya samu nasara a wannan aiki, sai kuma a duba yuwar fadada matatar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China