in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar SCO za ta kara taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya
2018-06-08 13:19:49 cri

Za a gudanar da taron karo na 18 na majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai (SCO) a tsakanin ranekun 9 zuwa 10 a birnin Qingdao na lardin Shandong na kasar Sin. Wannan ne karo na farko da aka shirya taron kolin, bayan habaka mambobin kungiyar. Jami'an diplomasiyya sun nuna cewa, kasashen India da Pakistan da suka halarci SCO a bara, sun kara sabon karfi ga kungiyar, za kuma su yi kyakkyawan tasiri ga ci gaban kungiyar.

To, masu sauraro, yanzu ga karin bayanin da wakiliyarmu Bilkisu ta hada mana.

Wannan taron kolin na Qingdao da za a kira a karshen wannan mako, ya kasance taron kolin na farko bayan an habaka mambobin kungiyar SCO. Ko da yake tun a shekarar 2005, kasashen India da Pakistan suka zama kasashe masu sa ido na kungiyar, amma har zuwa ranar 15 ga watan Yunin na bara, kasashen biyu sun halarci kungiyar a hukunce ne. Wannan ne ma karo na farko da aka habaka kungiyar tun bayan da aka kafa ta.

Jakadan kasar Sin dake India Luo Zhaohui yana ganin cewa, bayan kasashen India da Pakistan sun halarci kungiyar SCO, fadin kasashe mambobin kungiyar guda takwas na shafar sassan duniya na arewa har zuwa tekun Indiya. Adadin da ya kai kashi uku cikin biyar bisa na dukkan babban yankin Turai da Asiya, yawan mutanen dake yankin ya wuce biliyan 3.1, yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasa ya wuce dalar Amurka biliyan 17000, hakan ya sanya kungiyar ta SCO ta kasance mai iya kawo tasiri sosai a dandalin kasa da kasa. Gaskiya matakin na habaka mambobin kungiyar ya kara karfi sosai ga ci gabanta. Jakada Luo ya ce,

"Habaka mambobin kungiyar SCO ya samar da sabon karfi ga ci gaban kungiyar, ana sa ran ganin wani sakamako na a-zo-a-gani a kungiyar sakamakon yawan mutane, da yanki mai fadi, da yawan albarkatu da kuma babbar kasuwa. Baya ga haka, ana ta kara hadin kai da samu dama mai kyau a tsakanin kasashe mambobin kungiyar."

A matsayinta na abokiyar hadin kan kasar Sin bisa manyan tsare-tsare, a ko da yaushe daya tilo, kasar Pakistan na sa ran ganin wannan taron kolin da za a shirya a Qingdao. Jakadan kasar dake kasar Sin Masood Halid ya bayyana cewa, kungiyar SCO wani muhimmin dandali ne na inganta mu'ammala, da cudanyar cinikayya, da hadin kan tattalin arziki a yankin, ta samu babbar nasara a fannonin tsaro, siyasa, tattalin arziki da al'adu da dai sauransu. Bisa karuwar tasirin da kungiyar ke kawo wa duniya, wannan taron kolin na Qingdao zai nuna burin ci gaba na kungiyar a nan gaba. Jakada Masood ya ce,

"Kasar Pakistan sabuwar mamba ce ta kungiyar SCO, wannan ne karo na farko da za ta halarci taron kolin kungiyar bisa matsayinta na kasa mambar kungiyar. Muna fatan sanarwar Qingdao za ta nuna wa kungiyar burin da za ta cimma a nan gaba. Na yi imanin cewa, ta hanyar hadin kai tsakanin mambobinta, za a karfafa tasiri da muhimmancin kungiyar ta SCO a nan gaba."

Game da yanayin da ake ciki na samun farfadowar ra'ayin kariyar ciniki a duk fadin duniya, kungiyar SCO ta jaddada da manufar samun ci gaba cikin hadin kai a yayin habaka mambobin kungiyar, wannan na da daraja sosai. Babban daraktan gudanarwar kungiyar hadin kan masana'antu da cinikayya ta kasar India dake kula da harkokin kasar Sin, Atuk Dalakoti ya bayyana imanin cewa, yanzu kungiyar SCO na kasancewar misali ne na hadin kai a tsakanin kasashen duniya.

"A cikin shekaru biyu da suka wuce, an bullo da ra'ayin ba da kariyar cinikayya a wasu yankuna da dama a duniya, akwai wajibcin canja irin wannan hali. A gani na, taron kolin na Qingdao na kungiyar SCO na da muhimmanci kwarai. A yanzu haka kungiyar ta riga ta kasance wata kungiyar kasa da kasa dake shafar duk yankin Turai da Asiya. A nan gaba kuma, dukkan kasashen na Asiya da Turai za a iya hadin kai da su bisa wannan tsari na SCO."

A ganin babban sakataren kungiyar SCO Rashid Alimov, kasashen India da Pakistan muhimman kasashe guda biyu ne dake kudancin Asiya, suna da makomar tattalin arziki mai kyau da albarkatun al'adu. Kana kuma suna da fasahohi da yawa a fannonin kiyaye tsaron shiyya-shiyya, da yaki da ta'addanci. Shigar da kasashen biyu cikin kungiyar SCO na da amfani wajen gudanar da hadin kai a tsakanin kasashen kudancin Asiya, musamman ma kasashen nan biyu ta fuskokin tsaron yanki da yaki da ta'addanci. Ban da wannan kuma, za su kara haifar da tasiri ga sauran bangarori." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China