in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Pompeo zai ziyaci Koriya ta kudu da Sin bayan ganawar Trump da Kim
2018-06-08 11:06:50 cri

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bayyana cewa, bayan kammala taron ganawar Singapore a ranar 12 ga watan Yuni tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un, zai ziyarci kasashen Koriya ta kudu da Sin domin sanar da su irin abubuwan da za su wakana a lokacin ganawar.

Da yake jawabi a taron manema labarai, Pompeo ya ce zai kai ziyarar ne domin ganawa da takwarorinsa na kasashen Japan da Koriya ta kudu bayan kammala taron tattaunawar don yin aiki tare da su. Daga bisani zai yada zango a Beijing bayan taron na Singapore.

A sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta fitar ta ce, mista Pompeo zai ziyarci Seoul a ranakun 13 da 14 ga watan Yuni, sannan zai zarce Beijing a ranar 14 ga wata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China