in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a raba gonakin Afrika ta kudu, in ji shugaban kasar
2018-06-08 10:44:48 cri

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya bada tabbaci a jiya Alhamis cewa, akwai bukatar cigaba da shirin nan na kwace gonakin kasar ba tare da biyan diyya ba, yana mai cewa za kuma a raba gonakin ne ga mutanen da suka cancanta.

Shugaban kasar ya fadi hakan ne a lokacin bikin tunawa da kafuwar kungiyar Afrikanerbond wanda ya gudana a Paarl dake wajen birnin Cape Town, ya ce wadannan gonaki ba za su taba zama mallakin wasu rukunin mutane a kasar Afrika ta kudun ba.

Ita dai Afrikanerbond, ta kasance wata kungiyar siyasa ce, wacce daga bisani ta rikide zuwa jam'iyyar siyasa ta farko da aka kafa a kasar Afrika ta kudun a shekarar 1880. An kafa kungiyar ce da nufin bunkasa cigaban tattalin arziki, siyasa da kare martabar al'adun Afrika, musamman ma manoma 'yan Afrika.

Ramaphosa zai yi amfani da wannan dama wajen sake fasalin tsarin gonaki wanda Jam'iyyar ANC mai mulkin kasar ta aiwatar da shi.

Ya ce manufar gwamnatin kasar wadda Jam'iyyar ANC ke jagoranta ita ce, dukkan mutumin dake bukatar gona kuma ya cancanta dole ne a ba shi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China