in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Iraqi na neman a sake kidaya kuri'u da aka kada kan zaben majalisar
2018-06-07 13:17:35 cri

Majalisar dokokin Iraqi ta zartas da gyararren shiri na uku na dokar zabe na majalisar ta, bisa kuri'u da aka kada a jiya 6 ga wata, kuma tana neman a sake kidaya kuri'u da hannu, wato a maimakon amfani da na'ura kan dukkanin kuri'u da aka kada a zaben majalisar dokoki a sabon zagaye.

An ce, 173 daga cikin mambobin majalisar 328 suka halarci taro na musamman da aka kira a wannan rana. Bayan taron kuwa, an ba da wata sanarwa dake cewa, majalisar ta zartas da wannan gyararren shiri don tabbatar da adalci cikin zabe, saboda ganin akwai kuskure a cikin kidaya da aka yi da na'ura, za a sake kidaya wadannan kuri'u da hannu karkashin majalisar zabe mai zaman kanta, da bangarorin siyasa daban-daban na kasar.

Ban da wannan kuma, wannan gyararren shiri da aka yi amfani da shi cikin zabe a wannan karo kawai, ya nemi a yi watsi da kuri'un da masu gudun hijira da mutane dake kasashen waje suka kada.

Manazarta suna ganin cewa, sake kidaya kuri'un, mai yiwuwa ya yi tasiri ga babban zaben kasar, da ma kafuwar sabuwar gwamnatin kasar. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China