in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Musayar kwarewa tsakanin kasashe masu tasowa za ta taimaka wajen kawar da talauci
2018-06-07 09:26:32 cri

Jami'ai mahalarta taron shirin hukumar samar da abinci da raya aikin gona ta MDD FAO, sun bayyana cewa, yin musayar kwarewa ta hanyar hadin gwiwar kasashe masu tasowa babbar hanya ce da za ta taimaka wajen yaki da fatara da yunwa.

Shirin wanda aka yiwa taken "Kawar da talauci da yunwa da samar da abinci" wanda ya kunshi baje kolin hotuna, da yin zazzafar muhawara game da yadda za'a cimma nasarori a shirye shiryen samar da dawwamaman ci gaba na (SDGs) wanda ajandar samar da ci gaba nan da shekarar 2030 ta kaddamar da ita.

Kasashen Sin, Chadi, Kenya, Senegal, da Ghana suna mayar da hankali kan shirin, inda kowace daya daga cikin kasashen ta bayar da misalai game da irin dabarun da take amfani da su wajen aiwatar da wadannan shirye shirye.

A jawabinsa na bude taron, mataimakin babban daraktan shirin hukumar FAO, Daniel Gustafson ya bayyana cewa, kasar Sin tana aiwatar da shirin kawar da talauci nan shekaru 10 cikin sauri, wanda shirin na SDGs zai kare nan da shekarar (2030), kuma akwai abubuwa masu yawa da kasar Sin za ta yi musaya da sauran kasashen duniya ta fuskar irin nasarorin da ta cimma.

Jakadan kasar Sin a hukumar FAO Niu Dun ya bayyana cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa ga hadin gwiwar kasa da kasa, a daidai lokacin da kasar ke kokarin bunkasa ci gaban kanta.

Jakadan ya kara da cewa, hadin gwiwar kasashe masu tasowa karkashin shirin na FAO ya samar da wani dandali na tallafawa juna.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China