Kasar Sin na fatan harba karin taurarin dan Adam na binciken yanayi har guda 11 nan da shekarar 2025, a wani mataki na kara nazarin yanayi, da hasashe mai inganci, tare da fatan kaucewa mummunan tasirin annoba daga Indallahi.
Hukumar lura da sararin samaniya ta kasar Sin CNSA, ta bayyana cewa, taurarin dan Adam din da ake fatan aikewa sararin samaniya, za su yi kewaye ne a sassan falaki daban daban har guda 5.(Saminu)