in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin ya ce Xi amininsa ne abun dogaro
2018-06-06 11:08:24 cri

A gabannin ziyarar aikinsa a kasar Sin, haka kuma kafin halartarsa taron koli na shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwar Shanghai da za a kira a birnin Qingdao na kasar Sin, shugaban kasar Rasha Putin ya karbi intabiyu da shugaban babban gidan rediyo da telibijin na kasar Sin Shen Haixiong ya yi masa a ranar 31 ga watan Mayun da ya gabata, inda ya tabo magana kan huldar dake tsakanin Sin da Rasha, da makomar ci gaban kungiyar hadin gwiwar Shanghai tun bayan da ta samu habaka.

"Shugaba Putin, mun gode bisa karbar intabiyu ta musamman na babban gidan rediyo da telibijin na kasar Sin ya yi maka."

Wannan ne karon farko da shugaba Putin ya karbi intabiyu da manema labaran kasashen waje suka yi masa tun bayan da ya fara sabon wa'adinsa na shugaban kasar ta Rasha a farkon watan Mayun da ya gabata, shi ne kuma karo na farko da ya karbi intabiyu ta kafofin watsa labarai na kasar Sin a fadarsa ta Kremlin. Kafin intabiyun, da farko dai shugaba Putin ya nuna fatan alherinsa ga al'ummun kasar Sin baki daya, inda ya bayyana cewa, yana fatan kowanen iyalin kasar Sin zai ji dadin rayuwa a ko da yaushe.

Shugaba Putin ya ce, kasarsa tana dora muhimmanci matuka kan huldar abokantaka dake tsakaninta da kasar Sin, wato bisa matsayinsu na kasashe makwabta masu sada zumunta. Ya ce sassan biyu sun kafa huldar musamman dake tsakaninsu bisa tushen moriyar juna. A shekarar 2001, Sin da Rasha sun kulla "yarjejeniyar hadin gwiwar sada zumunta tsakanin kasashe makwabta", wadda ta kasance tushen kulla huldar dake tsakanin sassan biyu, haka kuma yarjejeniyar ta kara zurfafa huldar yadda ya kamata a fannonin gina kasa, da bautawa al'ummun kasashen biyu da sauransu. "Idan mun waiwayi maganar da shugaba Xi Jinping ya yi a gun taron wakilan JKS karo na 19, wato ya taba bayyana cewa, abu mafi muhimmaci shi ne kyautata rayuwar jama'a, to ta yaya za a cimma wannan burin? Hakika akwai hanyoyi da dama, amma buri kwaya daya ne tak, haka abun yake ma a Rasha, muna da buri irin wannan, wato kyautata rayuwar jama'a, babu zabi na daban, A don haka muna la'akari da cewa, nan gaba ta yaya za mu kyautata huldar dake tsakaninmu, ta yaya za mu kiyaye tsaro, ina ganin cewa, ya kamata mu yi kokari tare a fannonin kirkire-kirkire, da tattalin arziki ta yanar gizo, da fasahar kwayoyin halittu, da zaman jituwa a zamantakewar al'umma, da kuma kyautata tsarin tattalin arziki, ta haka za mu kara karfafa gine-ginen tattalin arziki a sabon zamanin da muke ciki. Ana iya cewa, muna da makoma iri daya. Na yi imani cewa, muddin dai mu sanya kokari, tabbas za mu samu ci gaba."

Bana ake shekaru biyar, tun bayan da kasar Sin ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya, a watan Mayun shekarar 2015, shugabannin Sin da Rasha sun daddale hadaddiyar sanarwa, inda suka hada shawarar ziri daya da hanya daya da yunkurin habaka hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakanin kasashen Turai da Asiya na Rasha. A cikin shekaru 3 da suka gabata, sassan biyu sun samu sakamako a bayyane kan aikin, musamman ma wajen samar da makamashi da sufuri da zirga-zirgar sararin sama da sauransu.

Yayin intabiyun, shugaba Putin ya yaba da shawarar ziri daya da hanya daya da shugaba Xi ya gabatar sosai, yana ganin cewa, shawarar tana da ma'ana wadda ke da makoma mai haske. Kana Putin ya jaddada cewa, kasarsa za ta nuna goyon bayanta ga shawarar, ita ma tana son kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin bisa manyan tsare-tsare. A shekarar bara da ta gabata, adadin cinikayya dake tsakanin Sin da Rasha ya kai dalar Amurka biliyan 87, adadin da ya karu cikin sauri, Putin ya dauka cewa, adadin zai ci gaba da samun karuwa yadda ya kamata.

Za a kaddamar da taron kolin kasashen mambobin kungiyar hadin gwiwar Shanghai a birnin Qingdao ba da dadewa ba, wannan karo na farko ne kungiyar ta kira taron koli tun bayan da ta kara shigo da sabuwar mambarta, Putin ya bayyana cewa, yanzu kungiyar ta riga ta zama kungiyar kasa da kasa, yana cike da imani ga ci gabanta, a sa'i daya kuma, ya jaddada cewa, "Ba mu son nuna kiyayya ga sauran kasashe, fatan mu kawai shi ne tabbatar da hadin gwiwa daga duk fannoni tsakanin kasashe mambobin kungiyarmu, wato mu samar da wajibabbun sharudda ga kasashe, yayin da suke gudanar da hadin gwiwa. Muna son cimma burin hakan ta hanyar kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninmu. Muna fatan hadin gwiwar zai kawo tasiri ga yanayin da kasashen duniya ke ciki, ina tsamanin cewa, tasirin hakan zai amfani daukacin kasashen duniya."

A gabannin gudanar da taron kolin Qingdao, Putin zai kai ziyarar aiki a kasar Sin bisa gayyatar da takwaransa na kasar Sin Xi ya yi masa. Tun daga shekarar 2013, har zuwa yanzu, shugabannin biyu suna yin ganawar kai tsaye har sau 20 dake tsakanin junansu lami lafiya, ganawar da ta jawo hankalin al'ummun kasashen duniya matuka. Yayin intabiyun, Putin shi ma ya takalo magana kan huldar dake tsakaninsa da tsohon amininsa Xi Jinping, inda ya bayyana cewa, Xi shugaba daya kacal wanda ya taba taya shi murnar ranar haihuwa, sun sha giya sun dandana abinci tare, a ganinsa, Xi amininsa ne abun dogaro. "A wancan lokaci, bayan da muka kammala aiki, shugaba Xi ya raka ni domin yin murnar ranar haihuwa, yana da kirki, kuma shi amini ne abun dogaro. Kamar sauran shugabannin kasashen duniya, yana son kara samun sakamakon aiki, ta yadda zai kyautata rayuwar al'ummun kasarsa. A ganina, Xi mai son tunani ne, akwai ban sha'awa idan ka tattauna batutuwan kasa da kasa da na tattalin arziki tare da shi."

Yayin taron kolin G20 da aka gudanar a birnin Hangzhou a shekarar 2016, Putin ya taba kawo wa Xi Jinping kyautar icekirim daga Rasha, lamarin da ya burge saura. Game da tsarabar da zai kawo ga shugaba Xi yayin ziyarar da zai kai yi a kasar Sin, shugaba Putin ya yi murmushi ya ba da amsa cewa, "Akwai su, amma siri ne yanzu."

A cikin zantawar tasu, Mista Shen Haixiong ya bayyana cewa, a cikin shirin "Babban labari tsakanin Sin da Rasha" wanda gidan rediyon kasar Sin CRI ke gudanarwa a kan shafin yanar gizo na Intanet, yanzu ana gabatar da shiri na musamman mai jigon "Wa zai zama mabiyan Putin". Sinawa masu shiga wannan aiki a Intanet ya kai miliyan 10 cikin mako daya. A madadin wadannan mutane, Mista Shen ya yi wa shugaba Putin tambayoyi da dama masu ban sha'awa. Mista Putin kuma ya amsa su daya bayan daya:

"Tambaya: A ganinka, wace kungiyar kwallon kafa za ta lashe gasar cin kofin duniya a wannan karo?"

"Amsa: Wannan babu tabbas, kungiyoyi da dama na da yiwuwar cimma nasara a gasar. Argentina da Brazil daga Latin Amurka suna da karfi."

"Tambaya: Wane dan wasan kwallon kafa kake kauna?"

"Amsa: A cikin dukkan 'yan wasa na Rasha da tarayyar Soviet, ina son Lev Yashin, 'yan wasa daga kasashen waje kuwa ina son Pele da Diego Armando Maradona."

"Tambaya: Wane irin wasan motsa jiki ka kan yi a kullum, tsawon yaushe kake gudanar da shi?"

"Amsa: Ina zuwa motsa jiki na sa'o'i biyu ko biyu da rabi a ko wace rana, ina motsa jiki da wasu na'urori ko wasan ninkaya, a wani lokaci ina 'wasan Judo. Kuma a wani lokaci na kan yi wasan hoki, amma ban kware a wannan fannin ba. "

A cikin zantawar tasu ta tsawo rabin awa, Putin ya kuma mayar da martani kan wasu manyan batutuwan dake jawo hankalin kasa da kasa, ciki hadda dangantakar dake tsakanin Rasha da kasashen yamma, da zirin Koriya da sauransu. Game da takunkumin da kasashen yamma suke sakawa Rasha, Putin ya ce, duk wani tarnaki da ake yi mata ba ya kan doka, kuma manufofi ne dake jawo illa ga bunkasuwar tattallin arzikin duniya, kana za su ta da hankali. Kaza lika ya yi fatan dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasashen yamma za ta samu sassauci bisa wani mataki da ya dace. Yayin da ya tabo maganar zirin Koriya, ya nuna cewa, matsayin da Rasha ke dauka kan wannan batu ya yi daidai da matsayin da Sin take dauka ko za a iya cewa suna da matsaya daya, wato ta kawar da makaman nukiliya a zirin, da kuma kwantar da hankali.(Jamila da Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China