Kasar Sudan ta gabatar da wani yunkuri na shirya taron ganawa tsakanin shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir, da madugun 'yan adawar kasar Riek Machar.
Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta bayyana cikin wata sanarwa jiya Talata, cewar wata babbar tawagar wakilai daga kasar Sudan ta ziyarci Juba a ranar Talata, inda ta gabatar da wasikar da shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya aikewa takwaransa na Sudan ta kudu Salva Kiir.
A cewar sanarwar, tawagar wakilan ta kunshi ministan harkokin wajen kasar Sudan Al-Dirdiri Mohamed Ahmed, da ministan albarkatun mai da iskar gas na kasar Azhari Abdul-Ghader Abdullah, da kuma babban jami'in hukumar tattara bayanan sirri na kasar Sudan Salah Abdallah.(Ahmad Fagam)