Shugaban ya yi furucin ne, gabanin taron shugabannin membobin kungiyar hadin gwiwar Shanghai ta SCO, wanda zai gudana tsakanin ranakun 9 zuwa 10 ga watan da muke ciki, inda shugaba Putin zai halarci taron gami da kawo ziyarar aiki a kasar Sin.
Dangane da batun zirin Koriya, shugaba Putin ya ce, kasar Rasha da kasar Sin suna da matsaya daya, bisa taswirar daidata al'amura a zirin da suka bayar. Ya ce kasar Rasha ta lura da yadda kasar Sin ta yi ayyuka da dama don sassauta yanayin da ake ciki a zirin Koriya, kana Rasha a nata bangare tana goyon bayan matakan na kasar Sin.
Haka zalika, mista Putin ya jinjina wa shugabannin kasar Koriya ta Arewa, kan yadda suka yanke shawarar daina gwajin makamai masu linzami, da na kare dangi.
Game da batun huldar dake tsakanin kasar Rasha da kasashen dake yammacin duniya, shugaba Putin ya ce, Rasha ba ta tsoron takunkumin da ake neman saka mata, duk da haka tana son kulla hulda mai kyau tare da kasashen yamma, ciki har da kasar Amurka.(Bello Wang)