in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar: wasu mata uku 'yan kunar bakin wake sun tada boma boman da suke da su a Diffa
2018-06-05 18:43:50 cri
A cewar wasu rahotannin da suka fito daga majiyoyin masu tushe, sun bayyana cewa wasu mata uku 'yan kunar bakin wake sun tada boma boman da suke dauke da su a unguwar Diffa Koura dake birnin Diffa a jiya Litinin da misalin karfe 10 na dare. Wadannan 'yan kunar bakin wake uku, daya daga cikinsu ta ta da nakiyarta a kusa da wata makarantar allo, dayan ma ta ta da nakiyarta a tsakiyar birnin, yayin da 'yar kunar bakin waken ta uku ta tada bom dinta a kusa da wurin da bom ta biyu ta fashe. Tuni dai jami'an tsaro suka killace wurare domin gudanar da bincike da samar da agajin gaggawa ga wadanda suka jikkata. A halin yanzu babu wani adadin da hukumomin wurin suka fitar game da wadannan hare hare amma ganau sun bayyana cewa a kalla mutane 9 suka mutu yayin da da dama suka ji rauni. Duk da cewar babu wata kungiyar da ta dauki alhakin wadannan hare-hare, wasu masu fashin baki na ganin hannun kungiyar Boko Haram a cikin hare-haren.. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China