in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu aikin jin kai biyu na kasashen Amurka da Jamus da aka sace a Nijar suna raye in ji shugaba Issoufou
2018-06-05 18:29:40 cri
Masu aikin jin kai na kasashen Amurka da Jamus biyu da aka sace a baya bayan nan a kasar Nijar suna nan a "raye" in ji shugaba Mahamadou Issoufou a ranar Litinin a yayin wata ziyarar aiki a birnin Paris na kasar Faransa. A cewarsa, ana da labarai da suka shafe su, an san cewa suna raye. Ana nan ana cigaba da kafa yanayi mai kyau domin ganin an sako su. In ji shugaban Nijar a cikin wata hira da kafar talabijin ta France 24.

Jorg Lange dake yi ma wata kungiyar mai zaman kanta ta kasar Jamus aiki an sace shi a ranar 11 ga watan Afrilu a yammacin kasar Nijar sannan aka kai shi zuwa arewacin Mali mai iyaka da Nijar. Yayin da a shekarar 2016, dan kasar Amurka Jeffery Woodke dake aiki a cikin wata kungiya mai zaman kanta an yi awon gaba da shi a garin Abalak dake yankin Tahoua mai tazarar kilomita 350 daga arewa maso gabashin Niamey, babban birnin Nijar. Shi ma an kyautata zaton yana kasar Mali a cewar wasu majiyoyin tsaron kasar Nijar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China