in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Putin ya rattaba hannu kan dokar yaki da takunkumai
2018-06-05 11:41:46 cri

Gwamnatin Rasha, ta ce shugaban kasar Vladimir Putin, ya rattaba hannu kan dokar da za ta ba shi damar mayar da martani kan takunkuman da Amurka da sauran kasashen da babu kyakkyawan dangantaka tsakaninsu, suka sanyawa mata.

Wata sanarwar da aka wallafa a shafin yada labarai na harkokin shari'ar kasar, ta ce dokar ta ba shugaban Rasha ikon haramtawa ko dakatar da hadin gwiwa da jama'a ko kamfanonin kasashen da babu kyakkyawar dangantaka a tsakaninsu.

Bisa tanadin dokar, za a iya hana jama'a ko kamfanonin kasashen yi gwamnatocin tsakiya da na yankunan Rasha hidimomi, da yin cinikayya da takwarorinsu na Rasha ko kuma shiga harkokin saye da sayar da kadarorin Rashar.

Sai da majalisar dokokin kasar ta amince da kudurin dokar kafin shugaba Putin ya rattaba hannu don mayar da ita doka.

Matakin, martani ne ga takunkuman da Amurka ta sanyawa daidaikun mutane da kamfanoni 38 na Rasha a watan Afrilun da ya gabata, ciki har da wasu manyan 'yan kasuwa 7 da manayn jami'an gwamnati 17, bisa zarginsu aikata abubuwa marasa kyau a fadin duniya. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China