in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Qatar na tallafawa sulhu tsakanin gwamnati da 'yan awaren Sudan
2018-06-04 13:25:50 cri
Kasar Qatar ta bayyana aniyarta, ta ci gaba da shiga tsakani game da rashin jituwa da ya dade tsakanin gwamnatin Sudan da masu dauke da makamai dake tada kayar baya a yankin Darfur.

A jiya Lahadi ne dai shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya bayyana hakan, yayin da ya karbi bakuncin ministan harkokin wajen Qatar din Mutlaq Al Qahtani a fadar sa dake birnin Khartoum.

Shugaban na Sudan dai ya zanta da Mutlaq Al Qahtani game da matakan cimma matsaya da 'yan tawayen, da ma yadda za a jawo hankalin su zuwa teburin shawara, karkashin tanajin wasu takardun bayanai masu lakabin DDPD da Qatar din ke marawa baya.

A nasa bangare Mutlaq Al Qahtani, ya fidda wata sanarwa mai tabbatar da wannan mataki, yana mai jaddada goyon bayan kasar sa game da sake komawa teburin tattaunawa. Ya ce burin Qatar shi ne cimma nasarar wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa.

A nata bangaren, Sudan ta bakin jami'in ta mai lura da batun yankin na Darfur Amin Hassan Omar, ta jaddada aniyarta ta komawa shawarwari. Omar ya ce ba da jimawa ba, za a gudanar da wani zama tare da wakilin kungiyar AU, domin kaiwa ga cimma matsaya ta wanzar da zaman lafiya tare da tsagin masu dauke da makaman, karkashin tanajin takardun bayanai na DDPD. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China