in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanan Afirka: Yawan kudin RMB da kasashen Afirka suka mayar na musaya da ake adanawa zai karu
2018-06-04 13:38:43 cri

Sakamakon gaggauta yin amfani da kudin Sin RMB a mataki na kasa da kasa, ya sa kasashe da yawa sun mayar da kudin RMB a matsayin kudaden su na musaya da ake adanawa.

Kwanan baya, mataimakan shugabannin manyan bankuna, da jami'an hada-hadar kudi na kasashe 14 na gabashi da kudancin Afirka, sun tattauna kan yadda za a yi amfani da kudin RMB, bayan da aka mayar da shi a matsayin na musaya da ake adanawa, sun kuma gano cewa, kamata ya yi a kara yawan kudin RMB a matsayi na musaya da ake adanawa, kuma a kara yin amfani da shi wajen musanyar bashi, da wasu huldodi da suka shafi kasuwanci, ko kudin musaya tsakanin kasa da kasa.

"Mun cimma daidaito kan cewa, kamata ya yi mu kara yin amfani da kudin Sin RMB. Yanzu lokaci ya yi gare mu."

Kwanan baya, a yayin taron kara wa juna sani da cibiyar nazarin tattalin arziki daga manyan tsare-tsare da kuma kula da harkokin hada-hadar kudi na gabashi da kudancin Afirka ta shirya, wadda ta kafa babban zaurenta a birnin Harare, hedkwatar kasar Zimbabwe, mataimakan shugabannin manyan bankuna da jama'an hada-hadar kudi na kasashe 14 na gabashi da kudancin Afirka sun tattauna kan yadda za a yi amfani da kudin RMB bayan da aka mayar da shi a matsayin musayar kudin da aka adana. Caleb Fundanga, darektan zartaswa na cibiyar ya bayyana cewa, "Kasashen Afirka da kasar Sin muna kara yawan cinikayya a tsakaninmu. Don haka babu shakka, kamata ya yi mu adana kudin Sin RMB a matsayin na musayar kudi, kana mu yi amfani da kudin na RMB a musanya ta bashi, ko wata huldar da ta shafi kasuwanci ko kudi tsakanin kasa da kasa, kamar yadda a baya muke yin amfanin da dalar Amurka da kuma kudin Euro."

Mista Fundanga ya kara da cewa, masu halartar taron suna ganin cewa, yin amfani da kudin RMB a musanya wani bashi da wata huldar da ta shafi kasuwanci ko kudi tsakanin kasa da kasa, da kuma biya wa bangaren Sin rancen kudi ta hanyar amfani da kudin RMB ya dace da moriyar kasashen Afirka. Sun kuma yi fatan cewa, nan gaba, za a kara yin amfani da kudin na RMB a musanya wani bashi da wata huldar da ta shafi kasuwanci ko kudi tsakanin kasa da kasa, yayin da suke yin ciniki da kasar ta Sin. "Alal misali, idan mun yi amfani da dalar Amurka, wadda kuma farashin musayarta na yanzu yake da tsada, mai yiwuwa mu yi asara wajen canjin kudi. Idan kuwa muka biya kai tsaye da kudin RMB, za mu iya magance irin wannan asara. Muna fatan za a kara yin amfani da kudin RMB a musanyar bashi, da huldar da ta shafi kasuwanci ko kudi tsakanin kasa da kasa, hakan da zai dace da moriyarmu."

Sakamakon gaggauta yin amfani da kudin Sin RMB a matakin kasa da kasa, ya sa kudin RMB ya kara taka rawa a matsayin musayar kudin da aka adana. Bisa tanade-tanaden da ke cikin "rahoton kasar Sin na aiwatar da manufofin kudi a watanni 3 na farko na shekarar 2018", an ce, kwarya-kwaryar kididdiga ta shaida mana cewa, manyan bankuna fiye da 60 na kasashen ketare sun tanadi kudin Sin RMB a matsayin musayar kudin da aka adana.

Mista Fundanga ya yi nuni da cewa, a yayin taron kara wa juna sanin, an tattauna kan yawan kudin RMB da kamata ya yi a adana a matsayin musayar kudin da aka adana. Ana kuma ganin cewa, nan gaba yawan kudin RMB zai karu a kasashen Afirka a matsayin musayar kudaden da aka adana. "Idan an kara yin amfani da kudin RMB, kamata ya yi a kara yawan kudin RMB a matsayi na musayar kudade da ake adanawa. Wasu na cewa, ya kamata yawan kudin RMB ya kai a kalla kashi 5 cikin dari bisa jimillar na musayar kudade da ake adanawa. Amma wannan mafari ne kawai. Sakamakon kara yawan ciniki da kasar ta Sin, ya sa wannan adadi zai karu zuwa kashi 10 cikin dari, har ya zuwa kashi 15 cikin dari. Galibi dai muna ganin cewa, adadin zai ci gaba da karuwa."

Mista Fundanga ya ce, masu halartar taron sun nuna sha'awa sosai kan hanyoyin da watakila za a bi wajen zuba kudin RMB bayan da aka mayar da shi a matsayi na musayar kudin da ake adanawa. Sun sa ran kara yin mu'amala da 'yan kasuwa, musamman ma kwararrun kasar Sin, domin kara samun bayanai masu nasaba da hakan. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China