Jerin gwanon wanda ma'aikatar lura da muhalli ta shirya, aka kuma gudanar karkashin kulawar hukumar REMA, daya ne daga ayyukan da mahukuntan kasar suka tsara, a matsayin bangare na bikin kare muhalli na kasa da kasa da zai guda a gobe Talata.
Da take tsokaci game da hakan yayin taron gangamin, babbar daraktan hukumar REMA Coletha Ruhamya, ta ce tattakin ya baiwa 'yan kasar damar nuna damuwar su, game da bukatar da ake da ita ta kyautata kiwon lafiya, da kare muhalli, ta hanyar dakile ci gaba da amfani da lejoji da ba a iya sake sarrafa su, da kuma daukar matakan kawo karshen gurbata muhalli da ledojin ke haifarwa.
Ruhamya ta kuma bukaci 'yan Rwanda, da su fara kauracewa amfani da irin wadannan ledoji masu gurbata muhalli, ciki hadda robobin da ake shan kayan kashe kishi da su, da kofuna, da farantai da butoci na roba. A maimakon su a cewar ta, su rungumi amfani da wasu nau'oin zuba kayayyakin na daban.
A ranar 29 ga watan Mayun da ya shude ne aka kaddamar da makon lura da muhalli na kasar Rwanda, wanda za a yi amfani da shi wajen gudanar da ayyuka, da taruka na musamman, domin fadakarwa, da aiwatar da matakan kare gurbatar muhalli ta hanyar ledoji. Cikin wadannan ayyuka kuwa hadda ziyarar duba yadda ake amfani da ledoji ba bisa ka'ida ba a dukkanin sassan kasar, tare da baje kolin yadda ake sake sarrafa leda. Ana kuma fatan kammala wannan ayyuka a ranar 5 ga watan nan na Yuni. (Saminu)