in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin gabashin Libya za ta goyi bayan gwamnatin rikon kwarya bayan taron Paris
2018-06-04 10:08:49 cri

Gwamnatin rikon kwaryar kasar Libya dake da ofishinta a gabashin kasar ta sanar a jiya Lahadi cewa, majalisar dokokin kasar Libyan dake gabashin kasar za ta goyi bayan gwamnatin rikon kwaryar ta hanyar shirya wani sabon tsari domin kawar da duk wani tarnaki wanda aka kafa karkashin yarjejeniyar da aka rattaba hannu a shekarar 2015 wanda MDD ta dauki nauyi.

Sanarwar ta zo ne kwanaki kadan bayan wani taron da aka gudanar a birnin Paris wanda ya hada jam'iyyun siyasar kasar ta Libya don tattauna hanyoyin da za'a bi don warware rikicin siyasar kasar.

A cewar sanarwar da gwamnatin ta fitar a ranar Asabar, shugaban majalisar dokokin kasar dake gabashi Agila Saleh, ya yi tattaunawa mai zurfi tare da shugabannin gwamnatin rikon kwaryar domin tattauna sabon tsarin wanda ya shafi batun ayyukan gwamnati da kuma babban bankin kasar Libyan.

Saleh ya ce, gwamnatin rikon kwaryar da babban bankin Libya za su aiwatar da wasu tsare tsare, da nufin kyautata yanayin rayuwar jama'ar kasar, wanda ya dace da sakamakon da aka cimma a taron na Paris, tare da wasu jami'an kasashen waje wanda firaiministan kasar Abdullah Thani ya jagoranci taron.

Sanarwar ta ce, za'a sanar da sabbin tsare tsaren ayyukan gwamnatin rikon kwaryar da na babban bankin Libyan ne bayan kammala azumin watan Ramadan wato zuwa tsakiyar watan Yuni.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China