Bangarorin biyu, sun yi musayar ra'ayi cikin yanani mai kyau, kan yadda za a aiwatar da ra'ayi daya da aka cimma a birnin Washington, da kuma batutuwan dake shafar aikin gona da makamashi da dai sauransu, inda aka samu babban ci gaba ta fuskar wannan aiki, sai dai ana bukatar bangarorin biyu su tabbatar da bayanai filla-filla game da batun.
Sai dai abun da ya kamata a lura da shi, shi ne, akwai wani sharadi ga yunkurin tabbatar da matsayar da aka cimma wajen shawarwarin da ake yi tsakanin Sin da Amurka, wato ya kamata kasashen 2 su yi kokarin dacewa da juna a tunaninsu, da kokarin magance tada yakin ciniki. Idan Amurka ta ci gaba da gabatar da manufar saka wa kasar Sin takunkumi a fannin cinikayya, to, dukkan sakamakon da aka samu wajen shawarwarin za su bi ruwa, wato ba za a aiwatar da su ba. Wannan shi ne matsayin da kasar Sin ta dauka, kana muhimmin batu ne da zai tabbatar da aiwatar da ra'ayi daya da aka cimma a Washington.(Maryam/Bello)