in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu jami'an kasashen Afirka sun gabatar da shawarar mayar da RMB kudin ajiyar su
2018-06-01 20:15:02 cri

A jiya Alhamis ne shugaban zartaswa, na cibiyar nazarin tattalin arziki da harkar kudi bisa manyan tsare-tsare, na kasashen dake kudu da gabashin nahiyar Afirka Caleb Fundanga, ya bayyana a Harare fadar mulkin kasar Zimbabwe cewa, yayin taron kara wa juna sani da cibiyarsa ta yi kwanakin baya bayan nan, wasu jami'an bankuna, da hukumomin kudi na kasashen Afirka, wadanda suka halarci taron sun gabatar da shawarar cewa, ya dace a yi la'akari da shawarar mayar da kudin Sin RMB, a matsayin kudin ajiyar kasashen shiyyar, haka kuma ya dace a kara habaka hada hadar sa a kasashensu.

Jami'an da suka zo daga kasashen Afirka 14, sun halarci taron da aka yi tsakanin ranekun 29 zuwa 30 ga watan Mayu. Shugaban zartaswar cibiyar Fundanga ya bayyanawa manema labaran Xinhua cewa, jami'an mahalarta taron suna ganin cewa, yanzu haka kudin da ake adanawa a bankunan yawancin kasashen shiyyar dalar Amurka da kudin Euro ne, amma irin wannan tsari ba ya biyan bukatun sauye-sauyen tattalin arzikin duniya, musamman ma a halin da ake ciki yanzu.

Kaza lika kasar Sin tana kara taka rawar gani wajen ci gaban tattalin arzikin duniya, haka kuma ta kasance muhimmiyar abokiyar cinikayya ta kasashen shiyyar, a don haka idan kasashen dake kudu da gabashin Afirka suka mayar da RMB a matsayin kudin ajiyar su, ko shakka babu za su ci gajiyar hakan.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China