in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cika shekara daya da kaddamar da layin dogon da ya hada Nairobi da Mombasa
2018-06-01 15:10:02 criA ranar 31 ga watan Mayun shekarar 2017 ne aka kaddamar da layin dogon da ya hada birnin Mombasa dake gabashin kasar Kenya da Nairobi, fadar mulkin kasar. Kamfanin gina hanyoyi da gadoji na kasar Sin shi ne ya dauki nauyin shimfida layin dogon, mai tsawon kilomita kimanin 480. Kana, wannan layin dogo ya kasance irinsa na farko da aka yi amfani da 'mizanin kasar Sin' wajen ginawa da kulawa da shi daga dukkanin fannonin a ketare.

Kaddamar da layin dogon da ya hada Mombasa da Nairobi na da muhimmiyar ma'ana a fannoni da dama, ciki har da bunkasa kasar Kenya da yankunan kewayenta, da gaggauta raya harkokin masana'antu a Afirka, da kuma kara aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya' a Afirka.

A nasa bangaren, mataimakin babban manajan kamfanin gina hanyoyi da gadoji na kasar Sin ko kuma CRBC a takaice, Li Quanhuai ya ce, wannan layin dogon, ba kawai canja zaman rayuwar al'ummar Kenya ya yi ba, har ma da taimakawa sosai ga bunkasar harkokin sufuri da kasuwanci a yankin gabashin Afirka.

A ranar 30 ga watan Mayun bara, kamfanin CRBC na kasar Sin da kamfanin kula da harkokin zirga-zirgar jiragen kasa na Kenya, suka rattaba hannu kan kwangilar gudanar da harkoki gami da kulawa da hanyar jirgin kasa da ya hada Mombasa da Nairobi, inda aka tanadi cewa, kasar Sin za ta samar da hidimar daidaita zirga-zirgar jiragen kasa, da kiyaye layin dogo, tare kuma da horas da ma'aikatan jirgin kasa na Kenya.

Tun farkon farawa, a kowace rana, ana samun zirga-zirgar jirgin kasa sau daya kawai a rana, tsakanin Mombasa da Nairobi. Daga baya, wato daga ranar 1 ga watan Nuwamban bara, aka kara samun zirga-zirgar jirgin kasan daga sau daya zuwa sau biyu a kowace rana. Baya ga Mombasa da Nairobi, jirgin yana kuma tsayawa a sauran wasu tashoshi bakwai, abun da ke samar da saukin tafiye-tafiye sosai ga mazauna wuraren.

Wani mutum mai suna Muhammed Sheriff ya ce, a lokacin baya su kan je Mombasa ta hanyar shiga cikin bas kadai, amma a halin yanzu, suna iya shiga cikin jirgin kasa, yana mai cewa, gaskiya akwai sauki sosai. Mutane na ganin cewa, ta hanyar shiga cikin jirgin kasa, ba ma kawai kyan muhallin waje za a iya gani daga cikin jirgin ba, har ma da samun damar mu'amala da sauran fasinjoji.

Har wa yau, kaddamar da layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi, wani labari ne mai kyau ga 'yan kasuwa dake yawan zirga-zirga tsakanin biranen biyu. Wani dan kasuwan Kenya ya ce, layin dogon ya rage yawan kudaden da yake kashewa wajen yin tafiye-tafiye tsakanin Mombasa da Nairobi da kashi 30 bisa dari ko ma fiye.

Har wa yau, wannan layin dogo ya taimakawa wasu mutane don cimma burinsu. Alal misali, wata budurwa ta ce ta samu aikin yi a jirgin kasa tsakanin Mombasa da Nairobi, inda take taimakawa mutanen dake da matsalar ji don kawo musu sauki. Ta ce, tana son wannan aiki sosai.

Sa'annan wani lauyan Kenya ya ce, layin dogo da aka gina tsakanin Mombasa da Nairobi, ba kawai taimakawa inganta ababen more rayuwar jama'ar kasar ya yi ba, har ma da taimakawa sosai ga canja tunanin mazauna wurin da dama, wato sun fahimci cewa, ashe ana iya kammala gina irin wannan katafaren aiki cikin kankanin lokaci, kuma ana iya tafiyar da harkokinsa ta hanyar da ta dace.

Bisa alkaluman da aka bayar, shimfida layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi ya amfanawa karuwar yawan GDP na Kenya da kashi 1.5 bisa dari, kuma ya samar da guraban ayyukan yi da yawansu ya kai 46000 a kasar. Za'a iya cewa, kaddamar da wannan layin dogo ya taimaka ga habakar tattalin arziki da wasu sana'o'i da dama a wurin, ciki har da sana'ar yawon shakatawa.

Wani manajan dake aiki a wani otel dake bakin tekun Mombasa, ya bayyana cewa, tun da aka fara zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin Mombasa da Nairobi, a halin yanzu a kowace rana, otel din ya kan tura bas-bas zuwa tashar karshe ta Mombasa don karbar baki masu zuwa yawon shakatawa. Ya ce, a halin yanzu, adadin yawan masu yawon bude ido da kan je otel dinsa a kowace rana ya karu sosai, ciki har da 'yan Kenya da dama, har ma da akwai wasu Sinawa.

A bara, yawan adadin mutanen kasashen wajen da suka je Kenya don yawon bude ido ya zarce miliyian 1.4, wanda ya karu da kashi 9.8 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2016. Dalilin da ya sa haka shi ne, gudummawar layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi gami da kyautatuwar tsarin zirga-zirgar jiragen sama, wadanda ke samar da sauki ga masu yawon bude ido.

Bugu da kari, wasu manazarta na ganin cewa, Kenya muhimmiyar mahada ce ta jigilar kayayyaki da hajoji a yankunan gabashin Afirka, don haka layin dogon da aka shimfida tsakanin Mombasa da Nairobi zai kara kyautata ayyukan jigilar kayayyaki tsakanin Mombasa da sauran wasu sassan gabashin Afirka, abun da zai amfana sosai ga ci gaban tattalin arziki a wurin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China