Shafin yanar gizo na Intanet na fadar shugaban kasar ya ba da labari cewa, a jiyan ne kuma a birnin Moscow shugaba Putin ya gana da sabbin shugabannin hukumomin tsaro,da sojoji, da hukumar leken asiri da sauran hukumomi.
Putin ya ce, babban aikin dake gaban hukumar tsaron kasar shi ne yaki da ta'addanci. Alkaluman kididdiga na nuna cewa, ko da yake ayyukan ta'addanci da aka aikata a Rasha sun dan ragu, amma ya kamata Rasha ta kara karfinta na yaki da ta'addanci, kuma kamata ya yi hukumomin da abin ya shafa su kara karfin bincike, da murkushe kungiyoyin 'yan ta'adda. Dadin dadawa, yana fatan hukumar tsaron za ta ci gaba da aiwatar da matakan yaki da leken asirin kasar da kiyaye tsaron iyakokin kasar da dai sauransu. (Amina Xu)