A jiya da safe ne kuma Mike Pompeo ya yi shawarwari da mataimakin shugaban kwamitin koli na jam'iyyar KWP ta Koriya ta arewa Mista Kim Yong-chol, inda ya bayyana imanin bangarorin biyu na bin hanyar da ta dace bayan shawarwarinsu. Kuma Amurka na fatan za a gudanar da ganawa tsakanin kasashen biyu kamar yadda aka tsara
Ban da wannan kuma, Mike Pompeo ya ce, Amurka ta bayyanawa Koriya ta arewa manufarta wato cimma kwakkwarar hanyar kawar da makaman nukiliya a zirin Korea. Ya kara da cewa, Amurka na fatan shawo kan Koriya ta arewa ta fahimci cewa, kasar za ta kara samun tsaro, idan har aka kawar da makaman nukiliya a zirin na Koriya, kuma tuni bangarorin biyu suka gudanar da jerin tattaunawa kan wannan batu. (Amina Xu)