in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin waje: Kamfanonin Amurka dake Sin sun amince da yanayin kasuwannin Sin
2018-06-01 10:50:00 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana a yayin taron manema labaru da aka yi a jiya cewa, kungiyar 'yan kasuwar Amurka ta fitar da farar takarda dake bayani game da kamfanonin Amurka dake Sin na shekarar 2018 cewa, kamfanonin Amurka sun amince da yanayin kasuwannin Sin.

Haka Sin za ta samar da wani yanayi na adalci, don jawo hankali masu zuba jari na kasashen waje da kare muradunsu yadda ya kamata bisa doka.

Rahotanni na cewa, kungiyar 'yan kasuwar Amurka ta ba da wani rahoto a ran 30 ga watan Mayu cewa, Sin tana kokarin bunkasa tsarin ciniki cikin 'yanci a duniya, kuma tana dukufa kan yin kwaskwarima a cikin gida. Kashi 6 cikin 10 na kamfanonin Amurka na daukar Sin a matsayin daya daga cikin wurare uku dake da kyakkyawan yanayi na zuba jari a duniya, ban da wannan kuma, kashi 1 cikin 3 na mambobinta sun habaka jarin da suka zuba a Sin fiye da kashi 10 cikin 100. Game da wannan adadi Madam Hua ta ce, galibin kamfanonin Amurka dake kasar Sin na nuna kwarin gwiwa sosai kan zuba jari a Sin, matakin da ya bayyana burin galibin kamfanonin kan manufar bude kofa da Sin take aiwatarwa da yanayin shigo da jari a Sin.

Dadin dadawa, Madam Hua ta ce, girman kasuwannin cikin gida na Sin zai ninka na Amurka sau uku ko hudu a nan gaba, kuma babu kamfanin da zai juya wa wannan kasuwa baya. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China