in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: 'Yan ci ranin Afirka na iya tallafawa bunkasar tattalin arzikin kasashen su
2018-05-31 21:17:52 cri

Wani rahoto na dandalin MDD mai lura da hada hadar cinikayya da samar da ci gaba ko UNCTAD a takaice wanda aka fitar a Alhamis din nan, ya nuna cewa 'yan ci ranin nahiyar Afirka, na iya tallafawa kasashen su na asali da dabarun ciyar da tattalin arziki gaba, da ma sauye sauyen da kasashen ke bugata don samun bunkasuwa.

Rahoton ya ce, a shekarar 2017 da ta gabata kadai, akwai 'yan asalin Afirka da yawan su ya kai miliyan 19, da suka yi zirga zirga tsakanin kasashen nahiyar, da ma wasu karin miliyan 17 da suka bar nahiyar zuwa wasu nahiyoyin, adadin da ko shakka babu, zai iya samarwa nahiyar ta Afirka zarafi na samun bunkasuwa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China