in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bukatun al'ummar Sin kan kayayyakin yau da kullum da aka shigo daga ketare yana da yawa
2018-05-31 12:07:14 cri

Kwanan baya, ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fidda rahoto game da kayayyakin yau da kullum da aka shigo dasu daga kasashen ketare, inda ta bayyana cewa, bukatu na al'ummar kasar Sin kan kayayyakin yau da kullum da ake shigo da su daga kasashen ketare yana da yawa, mutane sama da kashi 30 bisa dari suna da shirin sayan karin kayayyakin kasashen ketare. A sa'i daya kuma, kamfanonin kasar Sin suna da shirin habaka ayyukan shigar da kayayyaki daga kasashen ketare.

Ga karin bayani da wakilimmu Ahmad Fagam ya hada mana:

Bisa rahoton da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar mai taken "Nazari kan bukatu da samar da manyan kayayyakin bukatun yau da kullum", an ce, masu sayayya na kasar Sin suna da bukatu masu yawa kan hajojin da ake shigo da su daga kasashen ketare. Kuma bisa binciken da aka yi, an ce, adadin mutanen da suka biya kudade kan hajojin ketare da yawansu ya kai sama da kashi 30 bisa dari cikin dukkanin kudaden da suka kashe wajen sayayya ya wuce kashi 20 bisa dari, kuma mutane kimanin kashi 70 bisa dari suna ganin cewa, ingancin kaya ya kasance batu mafi muhimmanci da suke sa lura, a lokacin da suke sayan kayayyakin kwalliya, da dai sauran hajojin da aka shigo dasu daga kasashen ketare.

A shekarun baya bayan nan, hajoji masu inganci sosai sun ci gaba da samun karbuwa a kasuwannin kasar Sin. Cikin yankin hajojin ketare na wani babban kanti dake birnin Beijing, akwai mutane da dama da suke sayan kayayyakin yau da kullum da abinci. Masu sayayyar sun bayyana cewa, ingancin hajojin da aka shigo dasu daga ketare shi ne abu mafi janyo hankulansu.

"Diyata tana son kayan wasa kwarai da gaske, da kuma soyayyen dankali da aka shigo dasu daga ketare."

"Giya, kayayyakin da ake yin amfani da su a gida, iri-irin hajojin da aka shigo daga ketare suna da inganci, ana iya ci da kuma yin amfani da su ba tare da damuwa ba."

"Kayayyakin jarirai, kayayyaki sawa, kayan kwalliya, da kuma abincin jarirai. Ga abincin jarirai na kasar Japan, an raba su bisa watanni na jarirai, akwai sauki sosai."

Kuma bisa rahoton da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta samar, an ce, cikin rabin shekara mai zuwa, masu sayayya sama da kashi 30 bisa dari, suna shirya sayan karin kayayyakin ketare, kuma kayayyaki guda biyar suna kan gaba cikin jerin bukatunsu, wadanda suka hada da, kayan kwalliya, agogo da tabarau, kayayyakin mahaifiya da jarirai, motoci da kuma kayan ado. Mataimakin jami'in ofishin nazarin kasuwannin kasa da kasa na cibiyar nazarin hadin gwiwar ciniki da tattalin arzikin kasa da kasa na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Bai Ming yana ganin cewa, mutane suna kara mai da hankali kan ingancin kayayyaki, bisa karuwar kudaden shigarsu.

"A zamanin da, sabo da fararen hular kasar Sin basu da kudaden shiga masu yawa, shi ya sa, sun fi mai da hankali kan farashin kayayyaki. Amma, a halin yanzu, bisa kyautatuwar zaman rayuwarsu, sun fara mai da hankali kan ingancin kayayyaki, tabbas ne suna da bukatu na musamman kan ingancin kaya, da kuma tambari na kamfani na hajojin da aka shigo dasu daga ketare."

Karuwar bukatun masu sayayya ta sa kaimi ga kamfanonin da suke shigo da kayayyaki daga kasashen ketare, bisa rahoton da aka fidda, an ce, kamfanoni suna da matukar aniyar shigo da karin kayayyakin ketare. Kuma bisa binciken da aka yi kan hajoji nau'o'i 92, cikin shekara mai zuwa, kamfanonin Sin suna son kara adadin shigowar kayayyaki nau'o'i 34 daga cikinsu, ciki hada da 'ya'yan itatuwa, tufafin motsa jiki, abincin jarirai da yara, kayan kwalliya da dai sauransu.

A hakika, kasar Sin ta yi kokarin nuna niyyarta ta habakar shigo da kayayyaki daga kasashen ketare cikin shekarun baya bayan nan, kuma an yi ta rage kudin harajin kwastan na wasu hajojin ketare. Bisa kididdigar da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta yi, an ce, ya zuwa watan Janairu na shekarar bana, kasar Sin ta cire kudin kwastan kan hajoji nau'o'i sama da dubu 8. Misali, an rage kudin harajin kwastan da ake biya kan barasar inabi na Georgia da na Chile daga kashi 14 da kashi 30 bisa dari zuwa sifiri.

Dangane da wannan lamari, shugaban ofishin nazarin hadin gwiwar yankuna na cibiyar nazarin hadin gwiwar ciniki da tattalin arziki na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Zhang Jianping ya bayyana cewa, habaka adadin hajojin da za a shigo da su daga ketare zai biya bukatun al'ummar kasa, a sa'i daya kuma, zai iya taimakawa raya tattalin arzikin kasar.

"Bukatun al'ummar kasar Sin kan kayayyakin yau da kullum suna ta karuwa bayan da kasar Sin ta shiga cikin jerin kasashen dake matsakaicin matsayi wajen samun kudaden shiga. Ya kamata mu habaka aikin shigo da hajoji daga ketare domin biyan bukatun al'ummar kasa, a sa'i daya kuma, zai bada gudummawa wajen habaka bukatun al'umma, ta yadda za a tabbatar da karuwar tattalin arzikin kasar Sin. " (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China