in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta fadada bude kofa don kara jan hankalin masu zuba jari na kasashen waje
2018-05-31 09:10:49 cri
Kasar Sin za ta gabatar da wasu sabbin matakan da za su ja hankalin masu zuba jari na kasashen waje, domin kara bunkasa manufarta ta bude kofa da inganta tattalin arziki.

An cimma wannan matsaya ne yayin taron majalisar gudanarwar kasar da ya gudana jiya Laraba karkashin jagorancin Firaminista Li Keqiqng.

An kuma yanke shawarar cewa, za a kara fadada damar shiga kasuwar kasar, da daukar matakan soke wasu haramci da aka yi wa masu zuba jari na kasashen waje a bangarorin kera motoci da jiragen ruwa da kuma jiragen sama.

A cewar Firaministan, dole ne su yi kokarin alkinta matsayin kasar Sin na kasar da ta fi samun jari daga kasashen waje. Ya ce shirin kasar na bude Kofa ya taimakawa harkokinta cikin shekaru 40 da suka gabata.

Li Keqiang ya kara da cewa, kamfanonin kasashen waje masu zuba jari, sun bada gagarumar gudunmuwa ga bangaren fitar da kayayyaki. Kuma abu mafi muhimmanci shi ne, sun karawa kayayyakin kasar daraja tare da bunkasa sauye-sauye da kirkire-kirkire.

A cewar ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, jarin kasashen waje a kasar ya kai yuan biliyan 877.56, kwatankwacin kimanin dala biliyan 136.72 a 2017, adadin da ya karu da kaso 7.9 a kan na shekarun baya.

Har ila yau, taron ya yanke shawarar cewa, za a saukaka hanyoyin zuba jarin ne ta yadda zai dace da na sauran kasashen duniya.

Za a sake nazarin jerin abubuwan da aka haramtawa masu zuba jari na kasashen waje tare da fitar da shi kafin ranar 1 ga watan Yuli. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China