in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Maida alaka tsakanin Sin da Burkina Faso ya dace da moriyar kowa
2018-05-30 19:07:50 cri

Mai magana da yawun ofishin lura da harkokin yankin Taiwan, na majalissar zartaswar kasar Sin An Fengshan, ya ce dawo da alaka tsakanin Sin da Burkina Faso, mataki ne da ya dace, ya kuma yi daidai da bukatar al'ummar kasar dake yammacin Afirka.

An Fengshan ya ce, manufar kasar Sin daya tak a duniya, ta dace da kudurin da dukkanin sassan kasa da kasa suka amince da shi. Jami'in ya ce, daukar matakan zaman lafiya a yayin da ake fuskantar kalubalen alaka tsakanin sassa daban daban abu ne mafi dacewa, wanda ke iya haifar da ci gaba da zaman lumana, zai kuma samarwa al'ummun sassan biyu alfanu. Kana hakan ya dace da nasarar jami'iyyar DPP mai mulki a yankin Taiwan.

An Fengshan ya ja hankalin mahukuntan jam'iyyar DPP, da su amince da yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 1992 ba tare da bata lokaci ba, su kuma amince cewa, Taiwan da babban yankin Sin dukkanin su yankunan Sin ne wadda take daya tak a duniya, ta yadda zaman da ake yi na nuna wa juna yatsa dai sauya zuwa zaman lafiya da ci gaba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China