in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta sauke nauyinta yadda ya kamata a fannin kiyaye zaman lafiya a duniya
2018-05-30 13:27:09 cri

Ranar 29 ga watan Mayu, rana ce ta tunawa da cika shekaru 70 da MDD ta kadddamar da aikin kiyaye zaman lafiya. A bana ne, kuma kasar Sin ta cika shekaru 29 da shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya karkashin laimar MDD. Sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin sun gudanar da ayyuka a kasar Libya wadda ke fama da matsalar yake-yake, da kasashen Afirka inda suka yi yaki da cutar Ebola, sai kasar Sudan ta Kudu inda ake yin musayar wuta, da ma kasar Mali, wadda ke fama da matsalar 'yan ta'adda. Kasar Sin tana cika alkawarinta da kuma daukar hakikanin matakai na kiyaye zaman lafiyar duniya, da raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan dan Adam.

A ranar 28 ga watan Satumban shekarar 2015 ne, shugaba Xi Jinping na kasar Sin yayin da ya halarci taron koli kan batun kiyaye zaman lafiya a babban zauren MDD da ke birnin New York, ya yi karin bayani kan ra'ayin kasar Sin dangane da kiyaye zaman lafiya, inda ya yi nuni da cewa, zaman lafiya, buri ne na dukkan dan Adam kuma manufa ce da ake kokarin neman cimmawa. Kamata ya yi aikin zaman lafiya ya karfafa gwiwar mutanen da rikici ya shafa, ta yadda za su samu kyakkyawar makoma. Dole ne a inganta tsarin gudanar da aikin tabbatar da zaman lafiya, sa'an nan a hada aikin kare zaman lafiya da tsarin diflomasiya na yin rigakafin abkuwar rikici da kuma raya zaman lafiya tare, yayin da ake sulhuntawa, da kokarin yin jagoranci bisa shari'a, da sulhunta al'umma da kyautata zaman rayuwar jama'a a lokaci guda. Har ila yau, dole ne a inganta karfin daukar matakai cikin hanzari, a kokarin samun damar wanzar da zaman lafiya da ceton rayuka a kan lokaci.

Shugaba Xi ya kuma sanar da cewa, kasar Sin ta shiga sabon tsarin MDD na jiran kota-kwana a fannin kiyaye zaman lafiya, ta kuma kafa rundunar 'yan sandan kiyaye zaman lafiya da rundunar jiran kota-kwana na kare zaman lafiya mai kunshe da sojoji dubu 8. A watan Satumban bara, kasar Sin ta cika wannan alkawari. Kuma a daidai taron kolin da aka gudanar a shekarar 2015, kasar Sin ta lashi takobin kara tura ma'aikatan injiniya da na sufuri da kuma likitoci don shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya. Za kuma ta horas da ma'aikatan kare zaman lafiya na kasa da kasa dubu 2 nan da shekarar 2020, tare da gudanar da ayyukan kawar da nakiyoyin da aka binne a karkashin kasa guda 10. Sa'an nan za ta bai wa kungiyar Tarayyar Afirka tallafi kyauta da darajarsa ta kai dalar Amurka miliyan 100 ta fuskar aikin soja.

Alkaluman kididdiga na nuna cewa, a cikin shekaru 28 da kasar Sin ta shafe tana shiga ayyukan tabbatar da zaman lafiya karkashin laimar MDD, kasar Sin ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya fiye da dubu 35 don shiga ayyukan kare zaman lafiya karkashin shugabancin MDD guda 24. Yanzu haka sojojin kasar Sin kimanin dubu 2 da dari 5 suna kare zaman lafiya a sassa daban daban na duniya, wanda yawansu ya zarta na kasashe 5 da ke da kujerun dindindin a MDD.

A jajibirin ranar cika shekaru 70 da MDD ta fara aikin kiyaye zaman lafiya a duniya, ta kaddamar da wani hoton bidiyon musamman domin gode wa kasar Sin dangane da gudummowarta ta fuskar tabbatar da zaman lafiya.

Kafin António Guterres, babban sakataren MDD ya tashi zuwa kasar Sin domin halartar taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar Asiya ta Boao, ya zanta da manema labaru, inda ya ce, "Kasar Sin, wani muhimmin kinshigi ne a fannin kiyaye zaman lafiya a duniya. Musamman ma a halin yanzu da kasashen duniya suke fuskantar manyan kalubale, goyon bayan da kasar Sin take nunawa kan aikin kare zaman lafiya yana da muhimmanci. Baya ga tura ma'aikatan kiyaye zaman lafiya masu yawan gaske, haka kuma kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a fannonin kyautata tsarin MDD game da ayyukan kiyaye zaman lafiya, taimakawa MDD wajen inganta ba wa ma'aikatan kare zaman lafiya tabbaci da kyautata kwarewarsu, da kyautata yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa."

Yadda kasar Sin ta shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD gadan-gadan ya nuna yadda ta sauke nauyinta a matsayinta na babbar kasa, kana kuma ya nuna sahihancin kasar Sin da kuma aniyarta ta raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan dan Adam. Kamar yadda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya fada,"Duniyarmu wadda ke da girma sosai na fuskantar taroin matsaloli. Kasashen duniya na sa ran sauraren ra'ayin kasar Sin da kara sanin shirin Sin. Kasar Sin za ta biya bukatunsu. Wajibi ne mu tausayawa wadanda suke fama da wahalhalu na yake-yake, kana mu dauki mataki. Kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen duniya a koda yaushe, za ta kuma yi iyakacin kokarin taimakawa mutane, domin kara samun aminai. Na yi fatan cewa, kasashen duniya za su hada kai domin kara samun zaman lafiya a maimakon yake-yake, da yin hadin gwiwa a maimakon nuna kiyayya, a kokarin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan dan Adam." (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China