in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Sin zai bullo da fasahar zamani a fannin kudi a Afrika don bunkasa lantarki ta hanyar hasken rana
2018-05-30 10:48:33 cri
Kamfanin kasar Sin Shenzhen JCN New Energy Technology ya sanar a jiya Talata cewa, yana kokarin bullo da wani tsarin amfani da fasahar kudi ta zamani a Afrika wato (fintech), wanda zai yi amfani da ita wajen bunkasa samar da lantarki mai amfani da hasken rana ga magidanta masu karamin karfi.

Amdy Luo, daraktan ciniki na kamfanin, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi cewa, kamfanin ya riga ya samar da kayayyakin fasahar wadanda magidantan za su yi amfani da su wajen sayen na'urar lantarki mai amfani da hasken rana, kuma zasu iya biyan kudaden na'urar lantarkin da kadan kadan a kowane wata.

Luo ya ce, fasahar zata iya sada masu ta'ammali da lantarkin wajen biyan kudaden a duk wata.

Luo ya fada a lokacin bikin baje kolin albarkatun mai da iskar gas, da Afrika, da lantarki, da makamashi na shekarar 2018 cewa, idan masu amfani da lantarkin basu biya kudinsu na wata da ya dace su biya ba, na'urar zata daina aiki, kuma wannan zai rage irin fargabar da ake da ita na kin biyan kudaden daga bangaren abokan huldar kamfanin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China