Trump ya wallafa a shafinsa na Tweeter a jiya da safe cewa, Kim Yong Chol, mataimakin shugaban kwamitin tsakiya na Jam'iyyar 'yan kwadago ta Koriya na kan hanyarsa ta zuwa New York.
Donald Trump ya ce sun shirya muhimmin ayari domin tattaunawa da Koriya ta arewa, yana mai cewa, a yanzu haka, taruka na gudana saboda ganawar kasashen biyu.
A ranar Lahadin da ta gabata ne, Shugaba Trump ya tabbatar da cewa, wani ayarin jami'an Amurka ya isa Koriya ta arewa don tattaunawa game da shirya ganawa tsakaninsa da Shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un, wanda a baya aka shirya zai kasance a Singapore a ranar 12 ga watan Yuni mai Kamawa. (Fa'iza Mustapha)