Jens Stoltenberg ya kara da cewa, a watannin da suka gabata, mambobin NATO sun samu bambancin ra'ayi matuka kan wasu batutuwa, misali, yarjejeniyar yanayi ta Paris, yarjejeniyar nukiliya ta Iran da dai sauransu. A cewarsa, duk da wadannan bambamcin ra'ayi, kamata ya yi NATO ta nace ga gudanar da aikin tsaro cikin hadin kai tsakanin mambobinta, kuma mambobin kungiyar za su yi shawarwari kan matakan da za su dauka kan Rasha da hadin gwiwa da kungiyar EU a yayin taron kolin kungiyar da za a kira a watan Yuli a Brussels. (Amina Xu)