in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Iraqi na neman a sake kidaya kuri'un zaben majalisar
2018-05-29 13:13:57 cri

A jiya ne majalisar dokokin Iraqi ta zartas da wani kuduri, inda ta nemi a sake kidaya a kalla kashi 10 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben sabuwar majalisar dokokin kasar da hannu, wato maimakon ta injuna, ta yadda za a karfafawa masu kada kuri'a kwarin gwiwa.

Bayanai na nuna cewa, kididdigar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta fitar a ran 19 ga wata ta nuna cewa, jam'iyyar dake karkashin jagorancin shugaban darikar Shiite Moqtada al-Sadr ta sami kujeru 54 daga cikin 329, adadin da ya ba ta rinjaye. Amma, sauran jami'iyyu da kawancen siyasa sun yi zargin cewa an tabka magudi a zaben, don haka suka nemi a sake kidaya kuri'u da hannu. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China