in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Binciken kayan tarihi ya tabbatar da cewa al'adun kasar Sin na da tarihin shekaru 5000
2018-05-29 13:07:53 cri

Al'adun kasar Sin na daya daga cikin manyan al'adun duniya guda hudu wadanda ke da dogon tarihi. Menene asalin al'adun kasar Sin? Ta yaya ne suka kasance al'adu? Jiya Litinin, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya fitar da sakamakon wani babban aikin da aka gudanar na tsawon shekaru 15, wato bincike kan asalin al'adun kasar Sin gami da ci gabansu tun daga farko har zuwa wannan lokaci. Kungiyar masu gudanar da binciken sun gano cewa, yau shekaru 5300 da suka gabata, akwai al'adu a wurare daban-daban na kasar Sin. Za'a kuma rubuta wadannan sabbin sakamakon binciken tarihi cikin litattafan tarihi na makarantun midil na kasar Sin.

Kasar Sin, kasa ce mai dadadden tarihi, kuma ana maida hankali kan gudanar da bincike game da asalin al'adu a kimiyyance. Kasancewarsa wani muhimmin aikin nazarin al'adu na kasa, aikin nazarin asalin al'adun kasar Sin ya kunshi masana daga cibiyoyi gami da hukumomin nazarin kayan tarihi kusan 70 a duk fadin kasar, inda suka kammala bincike a matakai hudu daga shekara ta 2001 zuwa ta 2016.

A nasa bangaren, mataimakin shugaban hukumar kula da kayan tarihi ta kasar Sin, Mista Guan Qiang ya ce, ya zuwa yanzu, an samu muhimmin sakamako a wannan aiki. Mista Guan ya ce:

"Na farko, bayanan binciken kayan tarihi sun tabbatar da cewa, al'adun kasar Sin na da tsawon tarihi na shekaru dubu biyar. Kuma kungiyar masu gudanar da binciken na ganin cewa, yau shekaru kimanin 5800 da suka shige, al'adun kasar Sin sun samo asali a wasu wuraren kasar, ciki har da yankin Rawayen kogi, da tsakiya da kasan kogin Yangtze, da kuma yankin yammacin kogin Liao. Tun shekaru 5300 da suka gabata ne, aka fara samun al'adu a sassa daban-daban na kasar Sin."

Gudanar da bincike kan asalin al'adun kasar Sin, ba domin sanin a wace shekara al'adun kasar suka samu asali, ko kuma wane wuri ne asalinsu ba ne. Ainihin makasudin binciken shi ne, domin nazarin ta yaya al'adun suka kasance a kasar Sin, kana, ta yaya al'adu wurare daban-daban suke da alaka da juna. Aikin binciken ya tabbatar da cewa, al'adun kasar Sin na da salo iri-iri, Guan ya ce:

"Sakamakon binciken ya ce, yayin da al'adu suka fara samo asali a wurare daban-daban na kasar Sin, akwai bambance-bambance a tsakaninsu a fannonin da suka shafi muhalli, da tattalin arziki, da tsarin zamantakewar al'umma, da addini da kuma ra'ayin dan Adam. Wadannan wurare sun rika yin musanyar al'adu tsakaninsu inda suka hadu da juna har suka zama wata muhimmiyar al'ada mai suna Erlitou. Shi ya sa muna iya cewa, asalin al'adun kasar Sin gami da ci gabansu tun farko farawa shi ne, mu'amala gami da cudanyar al'adu iri daban-daban."

Binciken ya kuma gano wasu kwararan shaidu dake nuna cewa, al'adun kasar Sin na da tsawon tarihin shekaru dubu biyar, wato, an gano tsarin madatsar ruwa na farko da fadar gargajiya ta farko a duk duniya a yankin kasan kogin Yangtze, da rubutattun haruffan Sinanci na farko a yankin tsakiyar rawayen kogi da sauransu. Alal misali, an gina wani katafaren wurin tarihi a yankin Liangzhu na lardin Zhejiang na kasar Sin kimanin shekaru dubu biyar da suka gabata, a ganin Wang Wei, kana manazarci a sashin nazarin kayan tarihi na cibiyar nazarin ilimin zaman al'umma ta kasar Sin, wannan wurin tarihi ya shaida cewa, tun wancan lokaci, akwai rukunonin matakan al'umma. Mista Wang ya ce:

"Irin wannan gagarumin aiki, idan aka dauki 'yan kwadago dubu goma, za su kammala aikin gina shi a tsawon shekaru goma ko fiye. Shi ya sa a wancan lokaci, tattaro mutane masu tarin yawa don su yi wannan aiki, ba zai dogara kan wata kabila ko kuma wani kawance ita kadai ba, sam ba zai yiwu ba. Baya ga fadar sarakunan gargajiya da muka gano, an kuma gano wasu manyan kaburbura da aka gina kan wuraren ibada. A cikin wani kabari kuma, an gano kayayyaki masu daraja da dama, musamman wasu kayan dutse jade da suka jibanci addini, har da wani kayan dutsen jade na makami, wanda ya zama alama na mukami a bangaren soja. Don haka muna iya ganin cewa, akwai rukunonin matakan al'umma daban-daban tun wancan lokaci, inda madafun iko ko mukami ya samo asali. Wannan ya shaida cewa, tun a shekaru dubu biyar da suka gabata, akwai al'adun tsohuwar kasa a yankin kasan kogin Yangtze."

Har wa yau, aikin gudanar da bincike kan asalin al'adun kasar Sin ya gano cewa, yadda al'adun kasar suka samo asali da ci gaba, sun kuma aro wasu kyawawan abubuwa daga al'adun kasashe waje, ciki har da fasahar noman alkama daga yankunan yammaci gami da tsakiyar Asiya, da kuma fasahar kiwon dabbobi da sauransu. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China