in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara amfani da dokar kare bayanai mafi tsanani ta Turai
2018-05-28 13:22:54 cri

A ranar 25 ga wata ne, aka fara amfani da dokar kare bayanai ta Turai a duk fadin kasashe mambobin kungiyar ta EU, dokar da ake ganin ita ce mafi tsanani a tarihi. Game da haka, wani kwararre a fannin tsaron yanar gizo na kasar Sin yana ganin cewa, sabuwar dokar kare bayanai mafi tsanani za ta yi tasiri a duniya baki daya. A nata bangare ma, mai yiyuwa kasar Sin wadda ke ba da muhimmanci ga aikin kare manyan bayanai bisa manyan tsare-tsare za ta kara hanzarta tsara manufofi da ka'idojin kiyaye bayanai, don inganta hadin gwiwar kamfanonin Sin da na duniya a wannan fanni.

Ga karin bayani da wakiliyarmu Bilkisu ta hada mana.

Dokar kare bayanai ta Turai da aka fara amfani da ita a ranar 25 ga wata, ta kara karfin 'yancin kare muhimman bayanai masu shiga yanar gizo na kasashen Turai, ta kuma kara nauyin dake bisa wuyan kamfanoni a fannin kiyaye bayanai, tare kuma da kyautata tsare-tsaren sa ido da batun ya shafa. Game da haka, babban masani a fannin tsaron yanar gizo na kamfanin kimiyyar kayayyakin lantarki na kasar Sin, kuma mataimakin daraktan ofishin gwaji na gwamnatin kasar dake kula da ayyukan amfani da bayanai masu girma shehu malami Dong Guishan ya bayyana cewa, idan aka kwatanta da dokokin da, wannan dokar da Turai ke amfani da ita ta fi tsanani, kuma tana shafar fannoni masu yawa.

"Idan ba sa son su yi asarar wannan kasuwa dake kushe da mutane miliyan 500, da farko dole ne kamfanonin dake kasashen EU, da adukkan kamfanonin da suka shafi adana bayanai da na ba da hidima da ayyukansu suka shafi bayanan mutane ko kungiyoyin EU su martaba sabuwar doka. Saboda haka, dokar za ta yi tasiri ga duk duniya. Dokar mai kunshe da ayoyi 99, ko wannensu ya yi bayani dalla-dalla game da yadda dokar za ta kasance. Haka kuma an yi bayanin cewa, dukkan kamfanonin da ba su aiwatar da dokar ba, za a iya cin tarar su har dalar Amurka biliyan 5 zuwa 6. "

Dong ya jaddada cewa, ko da yake wannan sabuwar dokar ta shafi duniya baki daya, amma ba kamar yadda wasu kafofin watsa labaru suka tsammani na cewa, wai dokar babbar matsala ce ko masifa. A ganinsa, dokar ta nanata 'yancin sani da kare bayanai masu bayar da bayanai, kana ta tabbatar da bukatar nauyin kare bayanai dake wuyan ko wane bangare. Hakan zai sa kamfanonin samar da hidimar bayanai na kasar Sin su yi kwaskwarima a fannonin fasaha da gudanarwa da kuma ayyukansu.

"A ganina, kamata ya yi a kara kokarin hada kan fasahar a fannin bayanai mai girma. Kana a jaddada 'yancin sani da kare bayanai na masu samar da bayanai. Ina tsammani, neman ci gaba ta hanyar fasaha shi ne matakin da ya kamata kamfanonin ba da hidima da gudanar da bayanai masu girma su yi la'akari da shi. Baya ga haka, ya kamata wadannan kamfanoni su yi taka tsantsan kan matsalolin da suke fuskanta a fannonin gudanarwa da ayyukansu bisa sabuwar dokar."

Dong ya lura da cewa, a yanzu haka sauran kasashe suna taka tsantsan kan shiga wannan sabuwar dokar ta EU, a ganinsu, dokar ta sanya kasar Sin wadda ke mayar da raya ayyukan bayanai masu girma a matsayin manyan tsare-tsare, tana fuskantar kalubale a fannin yin kirkire-kirkire da amfani da manyan bayanai. Amma, a sa'i guda kuma ya jaddada cewa, kasar Sin na fuskantar dama da kalubale tare, mai yiwuwa ne za kuma ta samu dama mai kyau wajen ci gaban tsaron bayanai.

Idan aka kwatanta ta da dokar tsaron yanar gizo da dokar hukunta laifuffuka da kasar Sin ke gudanarwa a yanzu haka, dokar kare bayanai ta EU ta gabatar da bukatu mafi tsanani a fannin girmama 'yancin adana bayanai, ban da wanna kuma, ta na da tsanani sosai wajen tuhumar wadanda suka keta dokar. Dong yana ganin cewa, wannan ya ba da misali da yadda kamfanonin ba da hidimar bayanan kasar Sin ke tsara da kaddamar da manufofi da ma'aunin kare bayanai.

"A fannin tabbacin tsaron bayanai, kasar Sin ba ta da fasaha da tsarin gudanar da kare bayanai masu girma. A hakika, kasar mu tana iya koyo daga wannan dokar ta EU, don kyautata dokokin da batun ya shafa, da kuma tsara ma'auni a fannin, kana da raya fasaha da na'urorin kare bayanai, da kokarin yin nazari a kai, don tsara manufar kasa a wannan fannin. Wannan zai taimaka sosai ga hadin kan kamfanonin adana bayanai masu girma na kasar Sin da duniya baki daya." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China