in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta baiwa Nigeria dala miliyan 2 don tinkarar cutar kwalara data barke a jihar Yobe
2018-05-28 11:17:31 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, mutane 404 ne suka kamu da cutar kwalara, yayin da 15 daga cikinsu suka rasa rayukansu, tun bayan barkewar cutar a jihar Yobe dake arewa maso gabashin kasar a 28 ga watan Maris, yawan mace-mace ya kai kashi 3.7 bisa dari. Wannan ya sa MDD ta kebe dala miliyan 2 a matsayin tallafin jin kai don hana yaduwar cutar. Wadannan kudade za a yi amfani da su wajen samar da ruwa mai tsabta ga mutane sama da miliyan 1.6, da ingata yanayin tsafta, da kara kwarewar jamai'an kiwon lafiya a wuraren da cutar tafi kamari.

Jami'n kula da harkokin jin kai na MDD a Najeriya Edward Kallon ya bayyana cewa, wuraren dake da cunkoson mutane nan ne aka fi fama da barazana, sa'an nan rashin kyakkyawan kulawa zai iya sanya dubban mutane su rasa rayukansu. A cewarsa, hanya mafi dacewa ta hana yaduwar cutar ita ce kara ilimantar da jama'a game da matakan kariya, da gano da ba da magani ga wadanda suka kamu da cutar cikin hanzari. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China