in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron WHO tare da cimma sabuwar matsaya
2018-05-27 16:22:58 cri

A jiya Asabar, aka rufe babban taron hukumar lafiya ta duniya WHO karo na 71 wato (WHA), inda aka fidda sabuwar matsaya ta "triple billion" wanda hukumar ta WHO ta kuduri aniyar cimma nasarar samar da kiwon lafiya ga mutanen duniya biliyan uku nan da shekaru 5 masu zuwa, kamar yadda babban daraktan hukumar WHO Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya tabbatar da hakan.

A jawabin da ya gabatar na rufe taron, Dr. Tedros ya ce, an cimma matsayar samarwa al'ummar duniya biliyan 3 tsarin kiwon lafiyar ne kamar yadda aka amince cikin sabon kudurin na WHO a wannan mako. Ana fatar nan da shekarar 2023 za'a cimma nasarar shirin kamar haka: za'a samarwa karin mutane biliyan 1 a duniya tsarin kiwon lafiya na bai daya, za'a samarwa wasu mutanen biliyan 1 kariya ta hanyar ba da kulawar lafiya ta gaggawa, yayin da wasu mutanen biliyan 1 za su amfana da tsarin ingantaccen shirin kiwon lafiya.

Domin tabbatar da wannan buri na "triple billion", taron WHA ya bayyana wasu muhimman matakai wadanda za'a yi amfani da su, da suka hada da, kula da hanyoyin yaduwar cututtuka wadanda ba'a daukarsu ta hanyar iska wato (NCDs), wadannan nau'ikan cututtukan su ne ke sahun gaba wajen saurin halaka al'umma a duniya.

Mambobin hukumar WHO sun jaddada cewa, kasa da kasa za su himmatu wajen rage 1 bisa 3 na yawan mace macen da ake samu a duniya ta hanyar cututtukan na NCD, wanda ya yi daidai da ajandar shirin samar da dawwamamman ci gaba nan da shekarar 2030 wato (SDGs), musamman cututtukan da suka shafi ciwon zuciya, sankara, ciwon suga, da cutar da ta shafi hanyoyin numfashi, da inganta lafiyar kwakwalwa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China