in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya bukaci hadin gwiwar kasa da kasa kan shirin adana bayanai
2018-05-26 16:13:29 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci hadin gwiwar gamayyar kasa da kasa wajen yin musaya da kuma hadin gwiwa don bunkasa cigaban kamfanoni adana bayanai.

Xi ya yi wannan tsokaci ne a sakon da ya aike ga taron baje kolin kasar Sin na kasa da kasa game da babbar ma'ajiyar adana bayanai na shekarar 2018, wanda aka bude a yau Asabar a babban birnin Guiyang, na lardin Guizhou, dake shiyyar kudu maso yammacin kasar Sin.

Xi ya ce, yadda ake samun cigaban fasahar zamani cikin sauri a wannan karni, musamman a cigaban hanyoyin sadarwa ta intanet, da babbar ma'ajiyar adana bayanai, da dabaru irin na zamani sun yi matukar kawo gagarumin cigaban a fannonin zamantakewar alumma, da bunkasuwar tattalin arziki, da cigaban gwamnatoci, da fannin gudanar da sha'anin mulki, da kuma kyautata yanayin zaman rayuwar al'ummar kasashen duniya baki daya.

Ya ce kasashen duniya suna bukatar kara yin hadin gwiwa da junansu a fannin fasahar sadarwa wanda hakan wata babbar dama ce a fannin adana bayanai, kuma zai kyautata yanayin adana bayanan da magance kalubaloli a wannan fannin, musamman wajen kiyaye tsaron yanar gizo ga gwamnatoci.

Shugaba Xi ya ce, kasar Sin tana bada muhimmanci wajen cigaban babbar ma'ajiyar adana bayanai. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China