in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yaba da matakin Burkina Faso na yanke huldar diflomasiyya da Taiwan
2018-05-25 10:54:08 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta ce kasar ta yaba da matakin da Burkina Faso ta dauka na yanke huldar diflomasiyya da Taiwan.

Gwamnatin Burkina Faso ce ta sanar da kudurinta na yanke huldar diflomasiyya da Taiwan.

Kakakin ma'aikatar Lu Kang, ya ce abu ne da kowa ya sani cewa, a watan Oktoban 1971, yayin zama na 26 na zauren MDD, aka amince da kuduri na 2758, wanda ya bayyana gwamnatin Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, a matsayin halattacciyar gwamnatin dake wakiltar kasar Sin.

Manufar kasar Sin daya tak da aka amince da ita a cikin kudurin, ya zama abun da daukacin al'ummomin kasashen waje suka aminta da shi. Lu Kang, ya ce batu ne da ya shafi muhimman muradun kasar Sin da al'ummar Sinawa biliyan 1.3, wanda kuma shi ne tubalin da kasar Sin ke amfani da shi wajen kulla kawance da hadin gwiwa da kasashen waje.

Ya kara da cewa, suna maraba da Burkina Faso cikin kawancen kasar Sin da nahiyar Afrika, karkashin manufar kasar Sin daya tilo a duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China