in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 49 suka mutu yayin wani kwale kwale ya kife a tekun arewacin DRC
2018-05-25 10:48:42 cri

Gwamnan lardin Tshuapa Mboyo Iluka ya sanar a jiya Alhamis cewa, a kalla mutane 49 ne suka mutu bayan da wani kwale kwale ya kife a daren ranar Laraba a tekun Congo dake yankin arewa maso yammacin jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC.

Iluka ya ce, jirgin ruwan wanda ya tashi daga kauyen Monkoto zuwa Mbandaka ya kife ne a lardin Tshuapa. Kawo yanzu dai ba'a gano musabbabin faruwar hadarin ba.

A cewar wasu majiyoyi daga yankin, tuni aka aike da wata tawaga da ta hada da ministan harkokin ayyukan jin kai, da wasu manyan jami'ai zuwa inda lamarin ya auku domin gudanar da bincike kan wannan batu.

Sai dai a cewar hukumomi, galibi an fi danganta faruwar irin wadannan haddura na kifewar jiragen ruwa a tekun Kongo da rashin ingancin jiragen ruwan ko kuma daukar fasinjoji da suka wuce kima.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China