in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta fitar da kudin agajin jin kai ga yankin Sahel
2018-05-25 10:36:42 cri

Shugaban ofishin kula da agajin jin kai na MDD, Mark Lowcock, ya fitar da dala miliyan 30 a jiya Alhamis, domin taimakawa kasashe 4 na yankin Sahel, wadanda ke fuskantar matsananciyar fari da tsadar kayayyakin abinci da kuma tabarbarewar tsaro.

Sanarwar da ofishin ya fitar ta ce, dubban iyalai ne suka karar da abincin da suka adana, kuma a yanzu, suke rage yawan abincin da suke ci a rana.

Yaran da suka kai miliyan 1.6 ne ke cikin hadarin kamuwa da matsananciyar tamowa, inda mutane miliyan 5 kuma ke bukatar abinci da taimakon abun da za su dogara da shi, a wannan yanayi da ake tsammanin na gab da zama lokacin bazara mafi muni, idan abincin da aka adana ya kare kafin lokacin girbi na gaba.

Kudin da aka fitar daga asusun ba da daukin gaggawa na duniya, zai ba hukumomin ba da agaji damar kai wa ga mutanen da matsalar ta fi shafa, musammam a yankunan da ake noma da kuma kiwo da noma, a kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da kuma Mauritania.

Jimilar dala biliyan 1.37 ne ake bukata don taimakawa mutanen da suka fi rauni, a yankunan da farin ya shafa a Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da Niger da kuma Senegal. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China