in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron harkokin zirga-zirgar tauraron dan-Adan na kasar Sin a Harbin
2018-05-23 20:15:02 cri
Yau ne aka bude taron harkokin zirga-zirgar tauraron dan-Adan na kasar Sin karo na 9 a Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang.

Kwararru daga kasashe da yankuna da suka hada da Sin da Amurka da Rasha ne suke halartar taron na kwanaki uku, inda ake saran za su yi musayar ra'ayoyi kan amfani tauraron dan-Adam na zirgar-zirga da ayyukan hidima da sauran batutuwa.

Taron yana daya daga cikin manyan taruka da suka shafi tarukan harkokin zirga-zirgar tauraron dan-Adam na duniya guda uku. Tuni dai aka gudanar da taron shekara-shekara a birane Beijing, da Shanghai da kuma na shekarar 2010 da aka gudanar a birnin Guangzhou. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China