in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sana'ar sarrafa karafa ta kasar Sin ta samu ci gaba mai inganci cikin sauri
2018-05-22 10:28:52 cri

Mataimakin shugaban kungiyar masu sana'ar sarrafa karafa ta kasar Sin Mista Chi Jingdong ya bayyana a kwanan baya cewa, sana'ar ta su a nan kasar Sin ta shiga wani sabon matsayi na samun ci gaba mai inganci cikin sauri. Ya ce, wannan sana'a ta kai matsayin farko a duniya a fannin bincike kasa, haka ma kuma tace karfe da sarrafa shi. A nan gaba kuma, Sin za ta mai da hankali wajen samun bunkasuwa ta hanyar kirkire-kirkire a fuskar fasaha, da inganci, da ba da hidima.

Mista Chi Jingdong ya ba da wannan jawabi ne yayin da ya halarci taron koli da aka yiwa take da "Samun bunkasuwa mai inganci don raya sana'ar sarrafa karafa ta kasar Sin". Ya kuma bayyana cewa, a shekarun baya bayan nan, an gudanar da tsarin kayyade rarar kayayyakin da ake samarwa a wannan sana'a, kuma sana'ar ta samun bunkasuwa yadda ya kamata. A yayin da cikin shekarar 2017 kadai, yawan riba da kamfanonin fannin suka samu ta farfado da kashi 4.7 bisa dari.

A sa'i daya kuma, ya ce, ana kokarin daidaita tsarin samar da karfe, da yin tsimi makamashi, matakin da ya sa ake ci gaba da samun bunkasuwa ta hanyar kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha a wannan fanni. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China