in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayyana Ibrahima Kassory Fofana a matsayin sabon firaministan Guinea
2018-05-22 09:55:59 cri
Shugaban kasar Guinea Alpha Conde, ya bayyana Ibrahima Kassory Fofana a matsayin wanda ya nada mukamin firaministan kasar gabanin kafuwar sabuwar gwamnati, yayin wata sanarwa da aka watsa ta kafofin watsa labaran kasar.

Shugaba Conde ya yi amfani ne da wata dokar shugaban kasa wajen zartas da wannan mataki. Kaza lika ya umarci manyan sakatarorin ma'aikatun kasar, da su ci gaba da gudanar da ayyukan hukuma na yau da kullum, har zuwa lokacin da za a kaddamar da sabuwar gwamnati.

Kafin nadinsa a mukamin na firaminista, Ibrahima Kassory Fofana shi ne minista mai lura da harkokin zuba jari, da hulda da jama'a, da kuma ayyukan sassa masu zaman kan su na kasar. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China